Yaki da Isra'ila: Jerin Kasashen da Suka Gargadi Trump bayan Kai Hari a Iran
- Ƙasashe da ƙungiyoyi daga sassa daban-daban na duniya sun bayyana damuwa da goyon baya ga Iran bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliya
- Rasha, Saudiyya, China, Pakistan da Yemen sun bayyana adawa da harin, sannan sun nuna alamun goyon baya ga Iran yayin da ta ke fafatawa da kasar Israila
- A wannan rahoton, mun tattaro muku bayanan da kasashen suka yi, wanda ya kunshi gargadi kan yiwuwar bayar da agaji ga Iran da kuma neman sulhu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran ya janyo ƙarin rikici da faɗaɗa matsin lamba daga ƙasashen duniya.
A yayin da Amurka da Isra’ila ke nuna cewa harin ya dace, wasu ƙasashe da dama sun fito fili suna nuna damuwa da rashin amincewa da matakin.

Asali: Getty Images
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin wasu kasashen duniya da suka yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai tare da gargadin da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
1. Rasha: "Amurka ta karya dokokin duniya"
TRT Afrika ta wallafa a Facebook cewa ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana cewa harin da Amurka ta kai kan Iran ya sabawa dukkan ka’idojin ƙasa da ƙasa.
Rasha ta ce:
“Matsayar da Amurka ta ɗauka na kai hari kan ƙasar da ke da cikakken ‘yanci ya saba da dokokin duniya, kundin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙa’idojin kwamitin tsaro,”
Mataimakin shugaban kwamitin tsaro na shugaba Putin, Dmitry Medvedev ya ce wasu ƙasashe na iya ba Iran taimako wajen mallakar makaman nukiliya.

Asali: Getty Images
2. "Mun damu matuƙa da harin" - Saudiya
A daya bangaren, kasar Saudiyya ta bayyana damuwa mai zurfi dangane da harin da Amurka ta kai.
Rahoton Aljazeera ya nuna cewa Saudiyya ta ce:
“Masarautar Saudiyya na bin diddigin abin da ke faruwa a Iran da damuwa sosai, musamman kai hari kan cibiyoyin nukiliya,”
Saudiyya ta ce rikicin zai iya shafar zaman lafiya da tattalin arzikin duniya, musamman a fannin fetur da tsaro.

Asali: Twitter
3. China: "Harin soja yana haddasa rikici"
Gwamnatin China ta bayyana cewa tarihi ya nuna cewa hare-haren soja a Gabas ta Tsakiya kan haddasa rikici da tabarbarewar yankin.
China ta ce:
“Hare-haren soja sun daɗe suna haifar da matsaloli da ba a shirya ba, ciki har da rikice-rikice masu daukar lokaci da rushewar tsaro a yankin,”
Ana ganin kasar China za ta nuna damuwa sosai saboda dogaro da ta yi da yankin Hormuz wajen shigo da mai.

Asali: Getty Images
4. Pakistan ta ce harin Amurka ya jawo barazana
Ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ta ce harin ya biyo bayan na Isra’ila ne, kuma hakan zai iya haifar da ƙarin tashin hankali.
Sanarwar Pakistan ta kara da cewa:
“Pakistan na Allah-wadai da harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran… muna nuna matuƙar damuwa kan tasirin wannan lamari ga yankin gaba ɗaya,”

Asali: AFP
5. Turkiyya ta yi Allah wadai da harin Amurka
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da harin tana mai cewa zai iya jawo babban rikici a Gabas ta Tsakiya.
Turkiyya ta bukaci a tsagaita wuta nan take tare da komawa teburin sulhu domin shawo kan matsalar.

Asali: Getty Images
Bayan harin, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa:
“Wannan hari abu ne mai muni wanda zai haifar da illa mai dorewa… Iran na da haƙƙin kare kanta bisa tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da kare mutuncinta da iyakarta.”
An harbo jirgin leken asirin Isra'ila a Iran
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Isra'ila ta sanar da cewa an harbo wani jirgin leken asirinta a Yammacin Iran.
Rahotanni sun una cewa an harbo jirgin ne yayin da aka cigaba da gwabza fadan da ake yi tsakanin kasashen a ranar Litinin.
Sai dai duk da tabbatar da labarin, kasar Isra'ila ta ce jirgin ba shi da matuki kuma ba za a samu wasu bayanan sirri ba bayan faduwar shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng