Asiri Ya Tonu: Iran Ta Kama Ɗan Leƙen Asiri Isra'ila, An Rataye Shi gaban Jama'a

Asiri Ya Tonu: Iran Ta Kama Ɗan Leƙen Asiri Isra'ila, An Rataye Shi gaban Jama'a

  • Iran ta rataye Mohammad-Amin Mahdavi Shayesteh a ranar Litinin, bisa zargin leƙen asiri ga Isra'ila da kuma alaƙa da gidan talabijin Iran
  • Hukumar shari'ar Iran ta ce za ta gaggauta shari'o'in tsaro, bayan da aka kashe wani wakilin Mossad, Majid Mosayebi, a ranar Lahadi
  • Amnesty International ta nemi Iran da ta dakatar da duk wani zartar da hukuncin kisa, inda take zargin Iran na take hakkin wadanda aka kama

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iran - A ranar Litinin, ma'aikatar shari'ar Iran ta sanar cewa ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka samu da laifin leƙen asiri ga Isra'ila.

"An rataye Mohammad-Amin Mahdavi Shayesteh a safiyar yau saboda samunsa da laifin yi wa gwamnatin Zionist leƙen asiri a ƙasarmu," in ji ma'aikatar shari'ar.

Iran ta kama wani da laifin yi wa Isra'ila leken asiri, kuma ta rataye shi
Babban jagoran kasar Iran, Ali Hosseini Khamenei. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Iran ta rataye dan leken asirin kasar Isra'ila

Jaridar Times of Israel ta ce 'Zionist' shi ne sunan da Iran take kiran Isra'ila da shi, kalmar da ta samo asali daga masu fafutukar kafa kasar Yahudawa a karni na 19.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Rahoton da aka fitar ya nuna cewa gwamnatin Iran ta zargi Mohammad-Amin Shayesteh da cewa yana da alaƙa da Mossad, hukumar leƙen asiri ta Isra'ila.

An kuma same shi da laifin yin aiki tare da Iran International, gidan talabijin da ke watsa shirye-shirye da harshen Farisanci wanda ke London, kuma yana sukar gwamnatin Iran.

Iran na ɗaukar gidan talabijin a matsayin mai alaƙa da Isra'ila.

Tarihin hukuncin kisa kan masu leƙen asiri a Iran

Iran ta dade tana sanar da kamawa ko zartar da hukuncin kisa kan mutanen da take zargi da aiki da hukumomin leƙen asiri na waje, musamman na Isra'ila.

A ranar Lahadi, hukumomi sun yi alƙawarin hanzarta yanke hukunci kan irin waɗannan shari'o'in, inji rahoton ABS-CBN.

A wannan ranar ne ma'aikatar shari'ar ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Majid Mosayebi, wanda shi ma aka samu da laifin zama wakilin Mossad.

"Za a gaggauta shari'o'in da suka shafi tsaro, musamman waɗanda suka shafi goyon bayan gwamnatin kama-karya (Isra'ila)," in ji babban jami'in shari'a Gholamhossein Mohseni Ejei.
Kugniyar Amnesty ta bukaci Iran da ta dakatar da kashe mutanen da ake zargi da leken asiri ba tare da shari'a ba
Kungiyar Amnesty International, mai rajin kare hakkin dan Adam a kasa da kasa. Hoto: @AmnestyNigeria
Asali: Facebook

Matsayin Iran kan zartar da hukuncin kisa

Iran ce ta biyu a duniya wajen yawan zartar da hukuncin kisa bayan China, a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama ciki har da Amnesty International.

Da wuya ta fitar da hujjojin laifukan da aka samu waɗanda aka zartar da hukuncin kisa a kan su a bainar jama'a.

Kungiyar Amnesty International a sanawar da ta fitar shafinta na intanet, ta yi kira ga Iran da ta dakatar da duk wani shiri na zartar da hukuncin kisa ba tare da shari'a ba.

"Tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare kan Iran a ranar 13 ga Yuni, mahukuntan Iran sun kama dimbin mutane bisa zargin "haɗin gwiwa" da Isra'ila."

- Kungiyar Amnesty International.

Iran ta rataye dan leken asirin Isra'ila, Fekri

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Iran ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum mai suna Esmail Fekri, bisa zargin leƙen asiri ga Isra’ila.

An cafke Fekri tun watan Disamba na shekarar 2023, bayan binciken tsaro da jami’an Iran suka gudanar cikin ƙwarewa da zurfi.

Kotun koli ta ƙasar ta tabbatar da hukuncin ne bisa shaidun da suka haɗa da bayanan kwamfuta, kudaden da ya karɓa daga Mossad, da kuma amincewar Fekri da laifin da kansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »