Yadda Aka Kashe Mahaifin Ango da 'Yan Uwansa a Hanyar zuwa Daurin Auren Plateau
- Ana ci gaba da jimami kan kisan gillar da wasu gungun mutane suka yi wa masu zuwa ɗaurin aure daga Kaduna zuwa Plateau
- A yayin farmakin da ka kai wa mutanen, an hallaka mutum 12 har lahira yayin da aka jikkata wasu da dama
- Bayanai sun nuna cewa daga cikin mutanen da aka kashw har da mahaifin ango da wasu daga cikin ƴan uwansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Bayanai na ci gaba da fitowa kan kisan gillar da wasu mutane suka yi wa masu zuwa ɗaurin aure daga Kaduna zuwa Plateau.
Mahaifin ango tare da ƙaninsa na daga cikin waɗanda aka kashe yayin da suke tafiya ɗaurin aure a jihar Plateau a ranar Juma’a.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutanen guda 31 da ke tafiya a cikin wata babbar motar fasinja mai kujeru 18 mallakin jami’ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) sun fuskanci hari daga wasu gungun mutane a jihar Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Yadda aka kashe matafiya a Plateau
Babban limamin Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) na garin Mangu, Sheikh Suleiman Haruna, ya bayyana cewa waɗanda abin ya shafa mazauna garin Basawa ne a ƙaramar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.
Ya ce suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Pau da ke jihar Plateau domin halartar ɗaurin aure.
Mutum 12 daga cikin matafiyan sun rasa rayukansu, yayin da sauran mutum 19 da suka jikkata suke jinya a asibitin gwamnati na Mangu.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga harin, Ibrahim Umar, ya bayyana cikakken bayani kan abin da ya faru.
"Mahaifin ango da ƙaninsa duk an kashe su a cikin lamarin. Har ma da kawun ango shi ma an kashe shi."
"Angon asalinsa ɗan Zaria ne amma yana koyarwa a wata makaranta a yankin. A lokacin koyarwar ne ya haɗu da wata mace, suka yanke shawarar yin aure. Mun tashi daga Kaduna da kayan al’ada na aure, ciki har da goro da sauran kayayyaki."
“Mun bayyanawa waɗanda suka kai mana harin cewa mu ba ƴan asalin garin bane, kuma muna kan hanyarmu ta zuwa ɗaurin aure ne daga jihar Kaduna, amma sun ƙi fahimta. Dukkanmu ƴan uwa ne daga gari guda."
- Ibrahim Umar

Asali: Facebook
Sojoji sun kawo ɗauki
Wanda ya tsira daga harin ya yabawa sojojin da ke a kusa da wurin da lamarin ya faru saboda yadda suka gaggauta kawo ɗauki.
"Sojojin sun taimaka matuƙa. Sun zo suka cece mu. Da ba don saurin da suka nuna ba, da abin ya fi haka muni."
- Ibrahim Umar
Mahara sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mahara sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Plateau.
Maharan sun hallaka mutum huɗu ciki har da wani ƙaramin yaro ɗan wata tara a harin da suka kai a ƙaramar hukumar Bassa.
Mutanen da miyagun suka kashe suna kan hanyarsu ne ta zuwa wata kasuwa bayan sun ɗauko tumatur.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng