Dangote Ya Kara Farashin Fetur yayin da Yakin Iran da Isra'ila ke Kara Kamari
- Matatar Dangote ta ƙara farashin litar man fetur daga N825 zuwa N880, lamarin da ya haifar da fargabar hauhawar farashi a kasuwa
- Karin farashi na zuwa ne duk da cewa farashin danyen mai a duniya ya fara sauka yayin da ake cigaba da yakin ƙasar Iran da Isra'ila
- Ana sa ran sauyin zai shafi farashin gidajen mai, inda ake ganin zai haura N900 a wasu yankuna, musamman jihohin da ke nesa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matatar Dangote da ke Lekki a jihar Legas ta ƙara farashin sayar da fetur a daga N825 zuwa N880 a ranar Juma’a, 20 ga watan Yuni, 2025.
Masana na ganin karin ya yi yawa sosai, kuma yana iya zama barazana ga farashin gidajen mai da rayuwar yau da kullum ta al'umma.

Asali: Getty Images
Rahotannin da aka samo daga takardun harkokin mai da jaridar Punch ta gani sun tabbatar da karin farashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fara sauka bayan tashin da ya yi saboda yakin Iran da Isra'ila.
Wani abin damuwa shi ne yadda wannan karin zai shafi tsadar sufuri da rayuwa gaba ɗaya, musamman ga ‘yan Najeriya da ke fama da matsin tattalin arziki
'Yan kasuwa sun riga sun fara jan linzami kan karin farashi, inda ake hasashen zai kai har N950 a wasu jihohi.
Dangote ya koka rashin danyen mai a Najeriya
A cewar shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, matatar shi na dogaro sosai da danyen mai daga Amurka saboda ƙarancin isasshen kaya daga cikin gida.
Daily Post ta ruwaito cewa matatar za ta shigo da ganguna miliyan 17.65 na danyen mai daga Amurka tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli, 2025, inda aka riga aka karɓi ganguna miliyan 3.65.

Asali: Getty Images
Me ya jawo tashin farashin mai a Najeriya?
A ranar Talata, matatar ta dakatar da sayar da fetur ga dillalai tare da jinkirta fitar da albarkatun mai, abin da ya janyo hauhawar farashi a wasu rumbunan ajiya.
Dillalai da masu rarraba mai a Legas da wasu birane sun fara fargabar cewa Dangote zai sanya sabon tsarin farashi, lamarin da zai kai farashin fetur sama da yadda yake yanzu.
Kungiyoyin sun yi tir da karin kudin mai
Shugaban kungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce matakin na nuna yadda 'yan kasuwa ke cin moriya yayin da jama'a ke shan wahala.
Ya bayyana cewa da gaske ne bai kamata farashin ya wuce tsakanin N700 zuwa N750 ba idan aka yi la’akari da saukar da farashin danyen mai a duniya.
Dangote zai fara raba mai kyauta a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Aliko Dangote ya sanar da fara jigilar man fetur kyauta da abokan huldarsa a Najeriya.
Alhaji Aliko Dangote ya sanar da haka ne jim kadan bayan ya ce nan gaba kadan zai kawo gagarumin sauyi a harkar mai.
Kamfanin Dangote ya bayyana cewa zai samar da tankokin mai kimanin 4,000 domin safarar man fetur da dizil zuwa yankunan kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng