Zaben Abiola: Tinubu Ya Gane Kuskuren da Ya Yi, Ya Karrama Tsohon Gwamnan Kaduna
- Shugaba Bola Tinubu ya karrama Kanar Abubakar Dangiwa Umar da lambar CFR saboda gudunmawarsa a fafutukar dimokuraɗiyya Najeriya
- Tinubu ya ce ya manta da sunan Dangiwa a jawabin 12 ga Yuni, amma ya gyara kuskuren ta hanyar karramarsa a wani taro da aka yi a Kaduna
- Kanar Dangiwa, tsohon gwamnan Kaduna ne a mulkin soja, wanda ya zama fitaccen mai rajin sauyi, musamman bayan soke zaɓen 12 ga Yuni
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Shugaba Bola Tinubu ya karrama Kanar Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya) da lambar girmamawa ta 'Commander of the Order of the Federal Republic', (CFR).
Tinubu ya karrama Dangiwa Umar da wannan babbar lambar girmamawar ne saboda gudunmawar da ya bayar a fafutukar dimokuradiyyar Najeriya ta 12 ga Yuni.

Asali: Twitter
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da wannan karramawar ne a ranar Alhamis a yayin buɗe sabon asibiti mai gadaje 300 da cibiyar horar da sana'o'i a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Kanar Dangiwa Umar: 'Sojan dimokuraɗiyya'
Shugaba Tinubu ya bayyana Kanar Abubakar Umar, tsohon jami'in soja kuma mai sukar gwamnatocin baya a matsayin "sojan demokuraɗiyya."
Tinubu ya yarda cewa ya yi kuskure na manta sunan Kanar Dangiwa a cikin wadanda aka karrama a ranar 12 ga Yunin 2025, amma ya shaida cewa bai yi hakan da gangan ba.
"Bari in yi amfani da wannan damar don gyara wani kuskure da na yi. Daga cikin waɗanda na manta da su a lokacin jawabin 12 ga Yuni a majalisar dokoki ta ƙasa akwai Kanar Dangiwa.
"A yau, zan gyara wannan kuskuren da na yi ta hanyar karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasa ta CFR."
- Shugaba Bola Tinubu.
Kanar Dangiwa ya taba zama gwamnan Kaduna
An rahoto cewa Kanar Abubakar ya rike mukamin gwamnan jihar Kaduna a lokacin mulkin soja, kuma daga bisani ya zama mai fafutukar neman sauye-sauyen demokuraɗiyya.
Vanguard ta rahoto cewa Abubakar, ya kasance wani babban jigo a fafutukar da aka yi ta ganin an gudanar da zaɓe, da kuma adawarsu a kan soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yunin 1993.
Rashin saka sunansa a cikin waɗanda Tinubu ya karrama a ranar 12 ga Yuni, 2025, ya haifar da suka daga wasu kungiyoyin fararen hula da masu fafutukar kare dimokuraɗiyya.

Asali: Twitter
12 ga Yuni: Tinubu ya karrama mutane 66
Shugaba Tinubu ya ce lambar girmamawa ta ƙasa da ya ba Kanar Abubakar wata alama ce ta tunawa da rashin tsaro da jajurcewar da ya nuna a lokacin gwagwarmayar dimokuraɗiyya.
A ranar 12 ga Yuni, Tinubu ya bai wa mutane 66 lambobin girmamawa na ƙasa, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a dawo da Najeriya kan turbar dimokuraɗiyya.
Shugaban ya sanar da waɗannan karramawa yayin da yake jawabi a zauren haɗin gwiwa na majalisar dokoki ta ƙasa.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Shehu Musa Yar’Adua, Humphrey Nwosu, da Kudirat Abiola, waɗanda aka karrama bayan rasuwarsu saboda muhimmiyar rawar da suka taka.
An yi korafi kan wadanda Tinubu ya karrama
Tun da fari, mun ruwaito cewa, ce-ce-ku-ce ya barke bayan Shugaba Bola Tinubu ya karrama wasu fitattun jaruman da suka taka muhimmiyar rawa a fafutukar 12 ga Yuni.
Yayin da wasu suka yaba da wannan mataki, wasu kuma sun soki yadda Tinubu ya ki karrama wasu fitattun mutane da suka taka gagarumar rawa a gwagwarmayar.
Daga cikin wadanda aka karrama akwai Wole Soyinka, Femi Falana da Shehu Sani, yayin da kungiyar MOSOP ta bukaci gwamnati ta wanke sunan Ken Saro-Wiwa daga zargin kisa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng