Sojojin Najeriya Sun Gano Wurin Kera Bam a Borno, An Tashe Shi daga Aiki

Sojojin Najeriya Sun Gano Wurin Kera Bam a Borno, An Tashe Shi daga Aiki

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya watau NAF ta kai farmakin sama kan wani wuri da ake amfani da shi wajen hada bama-bamai
  • An kai harin a yankin Tumbuktu da ke jihar Borno bayan samun bayanan sirri cewa 'yan ta'adda suna kera makamai a wurin
  • Galaba da sojojin suka samu a kan 'yan ta'addan ya biyo wasu nasarorin da aka samu a kwanakin wajen wajen dakile 'yan ta'adda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta yi nasarar lalata wurin hada bama-bamai da kuma motocin yakin 'yan ta’adda a jihar Borno.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Sojoji sun samu bayanan sirri kan yan ta'adda a Borno
Sojojin Najeriya sun gano inda ake hada bam a Borno Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Dazu Punch ta wallafa cewa ya ce dakarun sojin sun halaka dimbin 'yan ta'adda a yankin Kwaltiri, da ke yankin Tumbuktu Triangle a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sojoji sun fatattaki yan ta'adda a Borno

Jaridar Vanguard ta ruwaito Ejodame ya bayyana cewa na’urorin leken asiri sun gani cewa akwai wani wuri da ake hada bama-bamai da kuma wasu motoci.

Ya kara da cewa nan da nan aka shirya jiragen yakin NAF a karkashin Operation Hadin Kai, suka kai farmaki suka lalata wurin baki dayansa.

Ejodame ya ce harin da aka kai ranar Laraba ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka tabbatar da ayyukan 'yan ta’adda a yankin.

Dakarun Sojoji sun yi nasara a jihar Borno

Jami'in sojin ya tabbatar da cewa ayyukan lalata wurin hada bama-baman ya kassara ayyukan yan ta'adda a Borno da kewaye.

Haka kuma ya ce wannan sako ne ga 'yan ta'addan cewa za a ci gaba da tarwatsa aniyarsu na hana jama'a zaman lafiya a jihar.

Ejodame ya ce:

“Wannan aiki babban darasi ne ga ‘yan ta’adda domin ya gurgunta karfin su na yaki, ya tarwatsa tsarin jagoranci da sadarwa da kuma hanyoyin kai dauki. Hakan ya haifar da rudani da karya masu gwiwa.”
Sojojin Najeriya sun kai hari kan yan ta'adda
Sojoji sun fatattaki sansanin hada bama-bamai a Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

“Harin da NAF ta kai ya tabbatar da azamar rundunar wajen ci gaba da rage karfin 'yan ta’adda da kuma tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.”

Harin na zuwa a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta dakile wani hari da 'yan ta'addan suka shirya masu da daddare da zummar mamaye sansaninsu a tafkin Chadi.

Jami'an Sojoji sun ragargaji ISWAP

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun sojin sama ta Najeriya sun kai wani farmaki a daijin Baikee, wani yanki da ke cikin Sambisa a jihar Borno.

Rahotanni sun ce sojojin sun yi nasarar tarwatsa sabon sansanin 'yan ta'addan ISWAP da ke tsaka da kulla yadda za su kai hare-hare yankunan Izge da kewaye.

An kai harin a ranar 13 ga Yuni, 2025, karkashin Operation Kalachen Wuta na rundunar Operation Hadin Kai da Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya jagoranta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »