Sulhu Ya Jawo Matsala, Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma Sama da 20 da Wasu Bayin Allah

Sulhu Ya Jawo Matsala, Ƴan Bindiga Sun Kashe Manoma Sama da 20 da Wasu Bayin Allah

  • Duk da an yi sulhu a wasu ƙananan hukumomi, ƴan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare tare da kashe mutane a jihar Katsina
  • Miyagun ƴan bindiga sun hallaka manoma aƙalla 20, da wasu mutane uku a sababbin hare-haren da suka kai yankin Kankara
  • Mazauna yankin sun ce suna zargin sulhun da aka yi a wasu yankunan ne ya sa ƴan bindiga suka koma wuraren da ba a yi sulhu ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - ’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 20, da wasu bayin Allah mutum uku da ɗan sintirin tsaro na al’umma guda daya watau C-Watch a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Kankara, daya daga cikin wuraren da ke fama da hare-haren ’yan bindiga a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Yan bindiga sun kashe manoma a Katsina.
Yan bindiga sun kashe mutane sama da 20 a Jihar Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa ƴan bindigar sun farmaki kauyukan kimanin biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yan bindiga sun shiga kauyuka akalla 5

“Kusan kwanaki shida da suka wuce, ’yan bindiga sun kai hari kan manoma a kauyukan Yargoje, Kwakware, Danmarke, Gidan Dawa da wasu daga Burdugau.
"Sun kashe manoma kusan 20, suka sace wasu kuma suka yi awon gaba da dabbobin da suke amfani da su wajen noma," in ji shi.

Wata majiyar ta daban ya shaida cewa a ranar Litinin, ’yan bindigar sun sake kai hari a kauyen Marmara duk a cikin Karamar Hukumar Kankara.

An kashe jami'an tsaro a Katsina

Ya ce yayin harin, ƴan bindigar sun yi artabu da dakarun C-Watch da ’yan sa kai watau JTF, kamar yadda The Cable ta rahoto.

A sakamakon hakan, sun kashe ɗan C-Watch guda daya da kuma jikkata ’yan JTF guda biyu a wajen kauyen.

Majiyar ta kara da cewa:

"Ƴan bindigan sun kuma kutsa cikin kauyen Marmara, inda suka kashe mazauna kauyen guda uku.”

Rahotanni sun ce a daren Litinin ɗinnan, ’yan bindigar sun sake kai hari a wasu ƙauyuka da ke gabashin Kwakware, inda suka sace mutane da dama tare da dauke dabbobi.

Gwamnan Katsina sanya da kayan dakarun C-Watch.
Yan bindiga sun kai hare-hare kan manoma da bayin Allah a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Ana zargin sulhun da aka yi ya jawo matsala

Wani mazaunin Kankara wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce hare-haren da ke faruwa a kwanan nan ba za su rasa nasaba da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da ƴan bindiga a ƙananan hukumomi da ke makwabtaka ba.

"Matukar ana cimma yarjejeniyar zaman lafiya a wuri guda, amma ba a aiwatar da hakan a sauran wuraren da abin ya shafa ba, to babu shakka ’yan bindigar za su kai hari inda ba a yi sulhu ba,” in ji shi.

Ƴan bindiga 12 sun baƙunci lahira a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar sheƙe ƴan bindiga 12 yayin da suka kai masu samame a jihar Katsina.

Ƴan bindigar sun baƙunci lahira ne a wani samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro da aka gudanar a ƙananan hukumomin Kurfi da Safana na jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Katsina.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »