Sojoji Sun Ragargaza Sansanin 'Yan Ta'adda, Sun Raunata Shugaban ISWAP, Albarnawi
- Dakarun Operation Hadin Kai sun kai hari ta sama inda suka lalata kadarori tare da kashe kwamandojin ISWAP da ke dajin Sambisa
- Rahotanni sun ce Shugaban kungiyar, Abu Musab Albarnawi, ya samu rauni yayin harin, amma har yanzu ba a tabbatar da halin da yake ciki ba
- An samu nasarar dakile taruwar yan ta'addan a wani sabon sansani da suka kafa da zummar kai mummunan hari kan mazauna Izge a Borno
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai wani gagarumin hari dajin Baikee da ke yankin Sambisa a jihar Borno, inda suka ragargaza sabon sansanin ’yan ta’addan ISWAP da ke wurin.
Harin da aka kai a karkashin Operation Kalachen Wuta na rundunar Operation hadin kai (OPHK) ya ta sama ya jawo mummunar barna ga 'yan ta'addan da suka hana jama'a zaman lafiya.

Asali: Twitter
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa rundunar OPHK da Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ke jagoranta sun ta kaddamar da wannan hari ne a ranar 13 ga Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
An tarwatsa sansanin ISWAP a Borno
Bayanai sun bayyana cewa an kai harin ne a dajin Baikee inda ’yan ta’addan ke taruwa a wani sabon sansani suna shirin kai farmaki kan bayin Allah, musamman na yankin garin Izge.
An bayyana cewa an yi harin ne cikin tsari tare da haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasa da na sama, ƙarƙashin jagorancin kwamandan sojin sama, Air Commodore UU Idris.
A cewar rahotanni, an lalata muhimman kayayyaki da kadarori da 'yan ta'addan suka mallaka, kuma an kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ta ISWAP.
Sojoji sun raunata shugaban ISWAP
Majiyoyin sirri sun bayyana cewa daya daga cikin fitattun shugabannin ISWAP, Abu Musab Albarnawi, ya samu mummunan rauni a fuskarsa sakamakon harin,.
Sai dai har yanzu babu tabbacin halin da yake ciki bayan ruwan wuta da suka sha ta sama da kasa daga dakarun Najeriya.

Asali: Facebook
Bayanan sun ce harin ya zo a kan gaba, ganin yadda ya ragargaza shirin su na sake kafa sansani da haɗuwa domin kai sabbin hare-hare.
Ana tsammanin yanzu haka, harin ya sa kungiyar ta shiga cikin rudani kuma ya rage masu karfin fada a ji da kai hare-haren ta'addanci a garuruwan dake Sambisa da kewaye.
ISWAP ta gwabza da Boko Haram
A baya, mun kawo labarin cewa wani rikici ya sake kunno kai tsakanin mayakan Boko Haram da na ISWAP a Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar kwamandoji da dama daga bangarorin biyu.
Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne daga farmakin da mayakan Boko Haram karkashin jagorancin Bakoura suka kai a sansanonin ISWAP da ke yankin karamar hukumar Abadam.
A ranar Juma’a, 14 ga watan Fabrairu, mayakan Boko Haram sun afkawa sansanonin ISWAP da ke yankunan Toumbun Gini da Toumbun Ali, inda aka yi artabun da ya jawo asarar rayuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng