Mayakan Boko Haram Sun Gamu da Azaba bayan Yunkurin Mamaye Sansanin Sojoji

Mayakan Boko Haram Sun Gamu da Azaba bayan Yunkurin Mamaye Sansanin Sojoji

  • Sashen sojojin ruwa na Operation Hadin Kai ya dakile wani hari da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai a sansanin rundunar
  • Rundunar ta bayyana cewa an gwabza da maharan har na tsawon sa’o’i biyu, inda sojojin Najeriya suka fatattaki 'yan ta’addan
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi niyyar kai harin don lalata wasu injina da gwamnatin Borno da saya da mamaye sansanin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Sashen sojojin ruwa na Operation Hadin Kai (OPHK) ya dakile wani hari da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai a sansanin rundunar ruwa .

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi kokarin mamaye sansanin da misalin 2.00 na dare a ranar Laraba da zummar kama iko da wurin.

Dakaraun Najeriya sun fatattaki Boko Haram
Sojoji sun dakile harin Boko Haram Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A sakon da rundunar sojin ta wallafa a shafin Facebook, ta ce maharan sun yi yunkurin lalata wasu sababbin injinan da gwamnatin jihar Borno ta sayo domin share hanyoyin ruwa a yankin Tafkin Chadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sai dai sun gamu da fushin sojojin da suka rike wuta, yayin da aka shafe tsawon lokaci ana gwabzawa kafin su saduda ganin alamun rashin nasara a arangamar.

Sojoji sun gwabza da 'yan Boko Haram

A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a shafin X, ta bayyana cewa dakarunta sun yi musayar wuta da maharan na tsawon sa’o’i biyu.

A cewar sanarwar:

“A wani aiki da aka tsara a tsakanin rundunonin kasa, ruwa da sama, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe 'yan Boko Haram/ISWAP da dama da suka yi yunkurin kutsa wa cikin sansanin ruwa na Lake Chad a Fish Dam da safiyar yau.”

Sojoji sun dakile harin Boko Haram

Sanarwar ta kara da cewa dakarun Najeriya sun ci karfin mayakan Boko Haram da suka yi kokarin kama ragamar sansaninsu da ke yankin tafkin Chadi.

Sanarwar ta bayyana cewa:

“'Yan ta'adda sun fara harin da 2.00 na dare da nufin lalata sababbin injinan Swamp Boggys da gwamnatin jihar Borno ta samar don tsaftace hanyoyin ruwa."
Sojojin Najeriya sun gwabza
Mayakan sun gamu da wuta daga sojojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A karin bayanin da rundunar ta yi, ta ce an samu aikin hadin gwiwa yayin da karin dakarun sojoji suka gaggauta kawo agaji daga Baga.

Sanarwar ta ce:

"Sai dai maharan sun gamu da cikas daga jami’an rundunar ruwa da kuma karin dakarun da suka iso daga Baga. Sun yi musayar wuta da su na tsawon sama da awa biyu kafin su ja da baya.”
“A yayin harin, ba su samu ikon mamaye sansanin ba, sai dai an lalata motar daukar marasa lafiya da wasu motocin rundunar guda biyu. Haka kuma, wasu dakaru sun samu raunuka.”

Rundunar soji ta bayyana cewa jiragen yakin saman Najeriya na ci gaba da kai farmaki a kan hanyoyin ruwa domin karasa ragargaza 'yan ta’addan da suka tsere.

Sojoji sun tarwatsa sansanin Boko Haram

A baya, mun wallafa cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun kai wani gagarumin hari ta sama a dajin Baikee da ke cikin yankin Sambisa, jihar Borno, tare da lalata sansaninsu.

Harin ya gudana ne a ranar 13 ga Yuni, 2025, karkashin Operation Kalachen Wuta, wani bangare na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), wanda ya janyo mummunar barna ga ’yan ta’addan.

Bayanai daga rundunar tsaro sun ce an lalata muhimman kayayyaki da kadarorin ISWAP, tare da kashe wasu daga cikin manyan kwamandojin kungiyar da raunata shugaban kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »