Ana tsaka da Rikicin Iran da Isra'ila, Minista Ya Hango Matsalar da Amurka Za Ta Jefa Najeriya
- Ambasada Yusuf Tuggar ya bayyana cewa matakin hana ƙasashen Yammacin Afirka shiga Amurka babbar matsala ce ga tattalin arzikin yankin
- Ministan harkokin ƙasashen wajen ya buƙaci Amurka ta canza tunani kan shirinsa na ƙaƙaba takunkumi kan Najeriya da duka mambobin ECOWAS
- Tuggar ya ce Najeriya da sauran kasashen Afirka ta Yamma na bukatar ƙulla hulɗar kasuwanci da Amurka idan aka yi la'akari da albarkatun yankin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Harkokin Waje na Najeriya kuma Shugaban Kwamitin Sulhu da Tsaro na ECOWAS, Yusuf Tuggar, ya hango matsala kan shirin Amurka na hana ƙasashen Yammacin Afirka shiga cikinta.
Yusuf Tuggar ya nuna damuwa kan sabon takunkumin biza da Amurka ta sanya wa ƙasashen yammacin Afirka, mambobin ECOWAS, a daidai lokacin da yaƙin Isra'ila da Iran ke ƙara tsanani.

Asali: Twitter
Ministan ya bayyana matakin a matsayin babbar matsala ga kasuwanci, diflomasiyya da ci gaban ƙasashen Yammacin Afirka gaba ɗaya, Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Yusuf Tuggar ya faɗi haka ne a jawabinsa nn buɗe taron Kwamitin Sulhu da Tsaro na ECOWAS karo na 54 da aka gudanar a Abuja ranar Laraba,
Tuggar ta hango matsala ga Najeriya, ECOWAS
Ministan ya yi gargadi cewa matakin na iya ruguza dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen Yammacin Afirka, musamman a wannan lokaci da yankin ke bukatar haɗin gwiwa a fannin tattalin arziki da tsaro.
A rahoton Vanguard, Ministan ya ce
“Abin takaici ne ƙwarai idan hakan ya tabbata, domin mu yanki ne da ke cike da damarmaki da albarkatu kuma a shirye muke mu kulla yarjejeniyoyi.
“Muna son yin kasuwanci da Amurka, amma matakin hana mu shiga ƙasar wani nau’i ne na cikas ga cinikayya a tsakaninmu.”
Ministan waje ya ce shirin Amurka kuskure ne
Yusuf Tuggar ya bayyana wannan mataki a matsayin kuskuren diflomasiyya, da asarar wata babbar dama, musamman idan aka yi la’akari da albarkatun da ke yankin ECOWAS.
“Muna da ma’adinai da da dama ciki har da abubuwan da ba ko'ina ake samun su ba kamar sindarin Samarium wanda aka gano a Jihar Bauchi, inda na fito,"
- Inji shi.
Yusuf Tuggar ya ba Amurka shawara
Ya kuma bukaci gwamnatin Amurka ta sake nazarin kan matsayar da ta ɗauka, yana mai cewa Yammacin Afirka na da dimbin abokan hulɗa da za ta iya dogaro da su.
“Kasashen ECOWAS da Amurka na da wata dama ta musamman ta haɗa kai da kulla yarjejeniya daidai da bukatu.
“Zamu kulla yarjejeniyoyi don ci gabanmu, tambayar ita ce: da wa zamu yi? Waye zai amfana ta hanyar ba jami’an gwamnati, masana, shugabannin kamfanoni da ‘yan kasuwa dama su rika zirga-zirga cikin ‘yanci?”
- Yusuf Tuggar.

Asali: Twitter
Wane mataki Amurka ke shirin ɗauka?
A halin yanzu, Shugaban Amurka, Donald Trump yana shirin sanya haramcin shiga ƙasarsa ga Najeriya da wasu ƙasashe da yawa, mafi yawansu daga Afirka.
Sabon tsarin zai buƙaci ƙasashen da abin ya shafa su cika wasu sharudda da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta gindaya cikin kwanaki 60.
Trump ta haramta ƙasashe 21 shiga Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana mutane daga ƙasashe 12 shiga ƙasar, ciki har da Iran.
Shugaba Trump ya ce an dauki matakin ne domin kare lafiyar mutanen Amurka daga haɗarin da ke zuwa daga waɗannan ƙasashe.
Matakin zai fara aiki ne daga ranar 9 ga Yuni, 2025, kuma yana ɗaya daga cikin alkawuran da shugaban ƙasar ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2024.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng