Tinubu Ya Bukaci Sauya Tsarin Mulkin Najeriya don Kafa 'Yan Sandan Jihohi
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi ya zama tilas domin fuskantar matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya
- Ya bukaci sauya kundin tsarin mulki domin ba jihohi damar kafa ‘yan sanda dominn inganta tsaro a yankunansu
- Shugaban kasa ya ce tsarin tsaro na yanzu ya gaza tinkarar kalubalen zamani kamar ta’addanci, fashi, da rikicin makiyaya da manoma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci sauya kundin tsarin mulkin Najeriya da nufin bai wa jihohi damar kafa ‘yan sanda.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne a Abuja yana mai cewa hakan ya zama wajibi duba da yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a fadin ƙasar.

Asali: Facebook
Daily Trust ta ce Tinubu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da majalisar wakilai ta shirya a Abuja, inda aka tattauna kan tsarin tsaron kasa da kuma bukatar sabunta kundin tsarin mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Za a samar da 'yan sandan jihohi inji Tinubu
Shugaban kasar wanda Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya wakilta, ya bayyana cewa tsaron kasa na bukatar sababbin hanyoyin warwarewa duba da sauye-sauyen zamani.
Ya ce:
“Batun kafa ‘yan sandan jihohi ba wai ra’ayi ba ne kawai yanzu.
"Yanzu haka manoma sun kasa zuwa gonaki, ‘yan kasuwa sun kasa yawo lafiya, al’ummomi sun koma dogaro da kansu wajen kare kansu,”
Ya bayyana kundin tsarin mulki na 1999 a matsayin tushen dimokuradiyya amma ya ce ya gaza fuskantar matsalolin tsaro na zamani.
Tsarin tsaro ya gaza - Shugaba Tinubu
Shugaban kasar ya kara da cewa sauyin yanayi a fannin fasaha da tsarin tsaro sun fi karfin yadda kundin tsarin mulkin yanzu ke tafiya.
Tinubu ya bukaci a sauya tsarin da ke sanya ‘yan sanda a karkashin dokar majalisa ta tarayya kawai, domin ba wa jihohi damar kafa nasu rundunar ‘yan sanda, matakin da zai inganta tsaro.
Yabo da suka kan ra’ayin kafa ‘yan sandan jihohi
Rahoton Punch ya nuna cewa matsayin shugaban kasar na goyon bayan ‘yan sandan jihohi ya dace da kiran da gwamnoni, sarakunan gargajiya da kungiyoyin farar hula ke yi a baya.
Sai dai Sufeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ta bakin CP Ohiozoba Ehiede, ya ce a maimakon kafa sabuwar runduna, a karfafa rundunar ‘yan sandan Najeriya da karin kudi.

Asali: Facebook
Amma shugaban kakakin majalisun dokoki na jihohi, Debo Ogundoyin, ya soki wannan ra’ayi, yana mai cewa matsalolin tsaro sun fi karfin wannan tsarin guda daya.
Ogundoyin ya ce:
“Dole ne mu duba tsarin tsaro na matakai da dama da ya hada da kafa ‘yan sandan jihohi domin kawo karshen matsalolin da ke addabar al’ummomi.”
Tinubu ya yabawa hadin gwiwar da ke tsakanin ofishin NSA da rundunonin soji, inda ya ce hakan ne ya kawo nasara kan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
An kama 'yan bindiga da kayan soji
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai gagarumin samame a jihohin Kaduna da Filato.
A jihar Kaduna, sojojin sun samu nasarar kama wani dan bindiga da aka samu sanye da kayan sojoji.
A jihar Filato kuma, dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar bankado wani waje da ake amfani da shi wajen boye makamai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng