Sheikh Gumi Ya Soki Kasashen Larabawa yayin da ake Ruwan Wuta tsakanin Iran da Isra'ila
- Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya zargi wasu daga cikin kasashen Larabawa ke kin tara makaman nukiliya
- Gumi ya bayyana cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya umurci Musulmi da su tanadi makaman zamani masu linzami domin kare kai daga barazana
- Ya yaba wa kasashen Iran da Pakistan bisa yadda suka kera makaman kare kai, yana mai cewa hakan ne ya kamata a yi domin kare rayuwar Musulmi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana rashin jin daɗinsa game da halin ko in kula da wasu kasashen Larabawa ke nunawa.
Haka kuma ya zargi wasu daga cikin kasashen da girman kai da rashin himma wajen kera makaman zamani masu linzami.

Asali: Facebook
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya hakikance cewa Allah Subhanahu Wa Ta'ala Ya ba da umarnin a tanadi irin wadannan makamai saboda ko ta baci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sheikh Gumi ya dira kan Larabawa
A rubutun da ya wallafa, wanda ya dauki hankalin jama'a, Sheikh Gumi ya bayyana cewa wasu daga cikin kasashen dake Gabas ta tsakiya sun tanadi makaman kare dangi.
“Allah -Subhanahu Wa Ta’ala- tuntuni Yayi umurni da tattalin kera makamai masu linzami, Pakistan Tayi, Iran Tayi amma abar kasashen larabawa sai girman kai da cin ‘shinkafa kaza’ ko takamar banza. Tir!”
Sheikh Gumi ya yaba wa kasashen Iran da Pakistan bisa yadda suka tsaya tsayin daka wajen kera makaman kare kai.

Asali: Facebook
Ya kuma caccaki wasu daga cikin kasashen Larabawa da ya ce sun fi mayar da hankali ne kan jin daɗin rayuwa da alfahari da takamar wofi.
Malamin ya jaddada cewa wajibi ne musulmi su kasance masu ƙarfafa kansu da kayan kare kai a wannan zamani da duniya ke cike da barazana.
Jama'a sun yi martani ga Sheikh Gumi
Sai dai wasu daga cikin wadanda ke bibiyar Sheikh Ahmad Gumi ta shafinsa na ganin Malamin na wadannan kalamai ne saboda yana jin haushin Saudiyya.
Aliyu Ibrahim Muhammad ya ce:
"Da bakin cikin Saudiyya za ka mutu! Ina so ka sani babu wani makami da Iran ta mallaka wanda Saudiyya ba ta da shi! Kuma ko yau duniya ta sahalewa Iran mallakar nukiliya, Wallahi Saudiyya sai ta mallaka! Kamar yadda lokacin da India ta ce sai ta mallaka ita ma Pakistan suka ce ba su yarda ba sai da suka mallaka tare! Allah ya shiryeka!"
Sanusi Faskari ya wallafa cewa:
"Allah ya saka masu da alkhairinsa na kula da masallatan harami masu alfarma Masallachin Haramin Makka da masallacin manzo a madina ya kare dukkan sharri."
Albani Bauchi Attanshawy ya ce:
"Allah ya kara wa saudiyyah daraja da girma, butulu kawai."
Saudiyya ta hana Sheikh Gumi shiga kasar
A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ba zai samu damar zuwa aikin Hajji a bana ba saboda wasu matsaloli.
Sheikh Gumi ya ce tun da farko an ba shi takardar izinin zuwa Hajji, amma daga bisani an nuna masa cewa ba a maraba da shi a Saudiyya, lamarin da ya bayyana rashin jin dadinsa.
Gumi ya bayyana jin dadinsa da yadda gwamnatin Najeriya ta nuna jajircewa wajen kare ‘yancinsa, ta hanyar tuntubar hukumomin Saudiyya domin kare dimokuraɗiyya da ‘yancinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng