Dangote zai Fara Raba Man Fetur Kyauta ga Abokan Huldarsa a Najeriya

Dangote zai Fara Raba Man Fetur Kyauta ga Abokan Huldarsa a Najeriya

  • Alhaji Aliko Dangote zai fara raba man fetur da dizel daga 15 ga Agusta 2025 a faɗin ƙasar nan ga abokan huldar shi
  • Rahotanni sun nuna cewa za a yi amfani da sababbin tankoki 4,000 da ke amfani da iskar gas na CNG domin raba man
  • An ruwaito cewa Dangote ya dauki matakin ne domin fatan tsarin zai rage farashin man fetur da farashin kaya a kasuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Matatar Dangote ta sanar da wani sabon shiri da zai canja yadda ake rarraba fetur da dizel a Najeriya.

Alhaji Aliko Dangote ya ce daga ranar 15 ga Agusta, 2025, zai fara raba fetur da dizel ga 'yan kasuwa, dillalan mai, kamfanoni, masana’antu da sauran masu bukatar mai da yawa.

Dangote zai fara raba mai zuwa jihohi
Dangote zai fara raba mai zuwa jihohi. Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da kamfanin Dangote ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wani babban abin burgewa a cikin shirin shi ne yadda Dangote ya shigo da sabbin tankokin man gas na CNG guda 4,000 domin saukaka rarraba man daga matatar.

Dangote ya kuma bayyana cewa rarraba man zai kasance kyauta ga dukkan masu saye daga matatar domin rage wahalar jigilar mai da kuma farashi.

Dangote zai rarraba mai kyauta a Najeriya

Dangote ya bayyana cewa za a tabbatar da cewa kowa da kowa zai amfana da wannan shiri, komai nisan wurin da yake.

Kamfanonin sadarwa, masana’antu, dillalan fetur da ma sauran masana’antu za su iya sayen mai kai tsaye daga matatar ba tare da tangarda ba kuma a kai musu kayan kyauta.

Baya ga haka, Dangote ya shirya gina tashoshin gas na CNG a sassa daban-daban na ƙasa tare da ƙara tankokin CNG guda 100 domin taimakawa rarraba mai cikin sauki.

Wannan zai taimaka wajen farfaɗo da tashoshin mai da suka tsaya, da ƙara samar da ayyukan yi, musamman a yankunan karkara.

Hakanan, Dangote zai bayar da damar basussuka ga masu sayen lita 500,000 na mai, inda za su iya samun karin lita 500,000 a rance na tsawon makonni biyu.

Ana fatana shirin raba man Dangote zai rage kudin fetur
Dangote ya bude kofar rajistar masu sayen mai daga matatar shi. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Dangote zai buɗe rajistar masu sayen mai

Kamfanin ya bayyana cewa daga 16 ga Yuni zuwa 15 ga Agusta za a buɗe rajistar masu sayen man domin tantance su.

Ana sa ran wannan tsari zai karfafa gwiwar masu zuba jari, rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kawo sauƙin samun man fetur a ƙauyuka da garuruwan da ke fama da ƙalubale.

Punch ta ce shirin zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da mai daga waje, da ƙarfafa ayyukan masana’antu da sauran manyan sassan tattalin arziki.

Dangote ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki – dillalan mai, kamfanonin sadarwa da masana’antu – da su shiga wannan sabon tsari domin amfanin kansu da ci gaban ƙasa.

Dan acaba ya yi murna da matakin Dangote

Wani dan acaba a jihar Gombe, Tukur Aliyu ya zantawa Legit cewa akwai alamar cewa matakin da Dangote zai dauka zai kawo saukin farashin mai.

Tukur ya ce:

"Idan hakan ta tabbata muna fatan samun sauki. Domin yafe wa gidajen mai kudin dako ba karamin sauyi zai kawo ba.
"Muna fatan hakan ya yi sanadiyyar sauke farashin mai a Najeriya."

Farashin mai zai iya tashi a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin Iran da Isra'ila ya jawo tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hakan zai sanya gwamnatin Najeriya kara samun kudin shiga dalilin fitar da danyen mai.

Sai dai masana sun ce tashin kudin danyen mai zai iya jawo karin farashin man fetur a gidajen mai a fadin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »