Gwamna Ya Fusata bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka kusan Mutum 200, Ya Sha Alwashi
- Ana ci gaba da jimami tare da alhini kan kisan gillar da wasu ƴan bindiga daɓake zargin makiyaya ne suka yi wa mutane a jihar Benue
- Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya fito ya yi Allah wadai kan mummunan kisan da ƴan bindigan suka yi wa mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Ya ba da tabbacin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya yi Allah-wadai kan hari da kuma kisan gilla da wasu makiyaya masu aikata laifuka suka kai wa mutanen ƙauyen Yelewata.
Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa babu wani dalili da zai halatta a ɗauki rayuwar wani mutum ba gaira ba dalili.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da bakin gwamnan, Tersoo Kula ya sanya a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ƴan bindiga dai sun kai hari a ƙauyen Yelwata inda suka cinnawa gidaje wuta tare da hallaka aƙalla mutum 200.
Me Gwamna Alia ya ce kan harin ƴan bindiga?
A cewar sanarwar mataimakin gwamnan jihar Benue, Barista Sam Ode, ya kai ziyara zuwa wajen da abin ya faru da safiyar ranar Lahadi bisa umarnin gwamnan.
Barista Sam Ode ya isar da saƙon cewa gwamnan ba zai huta ba, har sai an samu zaman lafiya a jihar baki ɗaya.
"Gwamna Hyacinth Alia na sane da kuma jin zafin raɗaɗin da kuka shiga sakamakon wannan hari da wasu miyagu ɗauke da makamai da ake zargin makiyaya ne suka kai muku."
"Gwamnatin jiha tana ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro na tarayya, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa matakan tsaro da kuma samar da mafita ta dindindin ga waɗannan hare-hare da suka zama ruwan dare."
- Tersoo Kula
An tura ƙarin jami'an tsaro a Benue
Sanarwar ta ce an fara shigowa da ƙarin jami’an tsaro masu ƙwarewa zuwa jihar Benue daga gwamnatin tarayya, haka kuma ana shirya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da suka fi fuskantar barazana.

Asali: Twitter
An kuma ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar rundunonin tsaro a jihar, kuma gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin dukkan mazauna jihar.
"A cikin yanayin zaman lafiya da haɗin kai, muna kira ga shugabannin addini, na gargajiya da na siyasa a faɗin jihar da su fadakar da matasa ƙarlashin kulawarsu kan gujewa taruka ko rikice-rikicen da ka iya haifar da mummunan sakamako."
- Tersoo Kula
Ƴan bindiga sun farmaki jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cwwa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan wani wurin da dakarun sojoji ke zama a jihar Benue.
Ƴan bindigan su yi artabu da jami'an rundunar tsaron jihar Benue waɗanda ke aiki a wurin a lokacin da suka kai harin.
Mummunan artabun da aka yi ya jawo rasa ran jami'an tsaro guda biyu yayin da kuma suka samu nasarar fatattakar ƴan bindigan.
Asali: Legit.ng