"Akwai Matsala," Mazauna Kano na Tsoron Fashin Waya Zai Gagari Kundila

"Akwai Matsala," Mazauna Kano na Tsoron Fashin Waya Zai Gagari Kundila

Matsalar fashin waya a jihar Kano ya fara sauya salo, yayin da gurbatattun matasa ke haura gidaje ko su balle shagunan jama'a, sun dabawa kashe mutane, sannan su dauke masu wayoyi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Matsalar fashin waya a Kano ta fara tayar wa da jama'a hankali, ganin yadda a cikin kwanaki kaɗan aka samu rahotannin kashe matasa da dama a fadin jihar.

A cikin wata tattaunawa da Ubaidah Muhd ta yi da Legit, ta shaida cewa ko a lokacin sallah, wasu matasa biyu sun tare wata mata tare da nuna mata wuka, suna bukatar ta mika wayarta.

Yan sandan Kano
Mazauna Kano sun shiga dimuwa kan matsalar fashin waya Hoto: Abdullahi Kiyawa
Asali: Facebook

A shafin Facebook na Premier radio, an ruwaito cewa yanzu haka ana makokin wasu matasa biyu a Sheka, da ke karamar hukumar Kumbotso, Kano, inda 'yan fashin waya suka kashe su a kusan lokaci guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

"Sai gwamnatin Kano ta farka," – Bakoji

A tattaunawa da Legit, Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya ya bayyana fargabarsa kan yadda fadan daba da fashin waya ke mamaye kwaryar birnin Kano da kewaye.

Kyaftin Bakoji ya ce:

"Abin takaici ne yadda fadan daba da rikice-rikicen matasa ke kara kamari a birnin Kano, musamman a cikin kwaryar birni kamar Kofar Mata, Kurna, Fagge, Dala, Jakara da Kurmawa, har ma da wasu yankuna kamar Dorayi da Unguwar Dabai."

Ya ce yanzu, da zarar an yi sallar Magrib, jama'a na shiga cikin razani, suna jin tsoron kai masu farmaki ko rasa rayuka.

Abin da ke ta’azzara daba a Kano

Kyaftin Bakoji ya ce bincikensu ya nuna cewa da yawa daga cikin matasan da ke cikin harkar daba da fashin waya ba su da ilimi kuma ba su da aikin yi.

A cewarsa, wannan na taka rawa matuka wajen dagula lamarin, baya ga shan miyagun kwayoyi da matasan ke yi.

Ya kuma ce ana zargin wasu ‘yan siyasa da bayar da kariya ga wasu daga cikin matasan da ke fashin waya, saboda dangantakarsu.

Yan sandan Kano
Bakoji ya shawarci yan sanda kan tabbatar da hukunta yan fashin waya Hoto: Abdullahi Kiyawa
Asali: Facebook

Ya ce:

"Iyaye da dama sun kasa sa ido kan ’ya’yansu. Wasu ba su san inda ’ya’yansu ke zuwa da dare, ko ma da rana ba. Yawancin matasan da ke wannan dabi'a na shan tabar wiwi, tramadol, codeine da sauran abubuwan da ke gusar da hankalinsu."

Ya kara da cewa rashin tabbatar da hukunci a kan wadanda aka kama da laifin fashin waya na kara wa wasu gwiwar ci gaba da aikata irin wannan laifi.

Kano: Masani ya bayar da mafita kan daba

Tsohon jami’in soja ya bayyana cewa rashin daukar matakan da suka dace kan matsalar tsaro a Kano zai iya dagula rayuwar jama'a gaba ɗaya.

Bakoji ya ce:

"Iyaye su tsawatar wa ’ya’yansu, su daina barin yara su rika yawon dare ba tare da sanin inda suke ba. Malamai kuma su rika wayar da kan jama’a kan illar wadannan miyagun dabi’u na yawon banza da fashi."

Ya ce akwai buƙatar wayar da kai ga dalibai da sauran matasa a kafafen yaɗa labarai kan illar fashin waya a birnin Kano da kewaye.

Bakoji ya kuma ja hankalin rundunar ’yan sandan Kano da su rika daukar mataki cikin gaggawa a kan duk wanda aka samu da laifin fashin waya a jihar.

Yan daba suna kwace a Kano

A baya, mun ruwaito cewa wasu 'yan daba sun bazama da yamma, gabanin sallar Magrib, a unguwar Kofar Nasarawa da ke cikin birnin Kano, inda suka tare jama’a suna kwace wayoyi.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun ce mamaki da firgici ya kama su ganin yadda aka fito gudanar da wannan aika-aika duk da cewa akwai ofishin ’yan sanda kusa da wurin.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu masu fashin suka kashe matasa biyu a cikin birnin Kano, yayin da jama'a ke cigaba da kokawa a kan matsalar daba a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

OSZAR »