Noma a Najeriya: Gwamnati Ta Ayyana kwanaki 3 na Azumi da Addu'a
- Ma’aikatar noma da samar da abinci ta kaddamar da azumi da addu’a na kwanaki uku domin neman taimakon Ubangiji kan matsalar abinci
- Wannan mataki ya biyo bayan ƙarin tsanani da Najeriya ke fuskanta dangane da rashin wadataccen abinci da hauhawar farashin kayan masarufi
- Za a gudanar da zaman addu’ar ne a babban zauren taro na ma’aikatar da ke Area 11, Garki, Abuja daga karfe 12:00 na rana zuwa 12:30 na rana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya ta sanar da fara wani shiri na musamman na addu’a da azumi na kwanaki uku.
Rahoto ya nuna cewa za a yi hakan ne domin neman taimakon Allah wajen fuskantar ƙalubalen rashin wadataccen abinci a Najeriya.

Asali: Twitter
Jaridar Tribune ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne a cikin wata takarda da ta fito daga ofishin daraktan kula da ma’aikata, Adedayo Modupe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran dukkan ma’aikatan ma’aikatar za su shiga cikin wannan ibada don samun nasara a shirye-shiryen gwamnati na tabbatar da tsaro a harkar abinci.
Takardar da aka fitar ranar 11 ga Yuni, ta bayyana cewa zaman addu’ar zai gudana ne bisa taken “Shiga cikin addu’a don kare ƙasa da neman cigaba.”
Za a fara azumin ranar 16 ga Yuni
A cewar sanarwar, za a fara azumin ne a ranar Litinin, 16 ga Yuni, sannan a ci gaba da shi a ranakun 23 da 30 na watan Yuni.
Ma’aikatar ta ce an shirya yin zaman addu’ar a babban dakin taro da ke hedikwatar ma’aikatar a Area 11, Garki Abuja, daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa 12:30 na rana.
The Cable ta rahoto cewa za a yi addu'o'in ne a kowanne daga cikin ranakun da aka kayyade domin yin azumi.
Sanarwar ta ce:
“An bukaci dukan ma’aikata su zo suna azumi domin neman shiriya da taimakon Allah a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi don magance matsalar karancin abinci a Najeriya,”
Ma'aikatar noma: Dalilin azumi da addu'o'i
Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da karancin abinci sakamakon abubuwa da dama da suka hada da sauyin yanayi, rashin tsaro da kuma hauhawar farashi.

Asali: Facebook
Gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙari wajen kaddamar da shirye-shirye daban-daban don inganta noman cikin gida da rage dogaro da abinci daga ƙasashen waje.
Sai dai har yanzu, farashin kayan masarufi kamar shinkafa, masara da gero na ci gaba da zama barazana ga rayuwar al’umma, musamman talakawa.
Masu casar shinkafa sun tafka asara
A wani rahoton, kun ji cewa masu casar shinkafa da manoma sun tafka asara a jihohi daban daban a fadin Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan karyewar farashin shinkafa saboda shigo da ita da ake daga ketare maimakon dogaro da ta gida.
Masu casar shinkafa sun bukaci gwamnatin tarayya ta dawo da wasu tsare tsare da gwamnatin Buhari ta kawo da suka shafi noma a Najeriya.
Asali: Legit.ng