Sheikh Ya Tayar da Ƙura kan Zargin Bautar Gumaka a Arewa, an Yi Masa Barazana
- Wani limamin Musulunci, Dr Sharafdeen Gbadebo Raji, ya fusata mutane da maganganunsa kan zargin bautar gumaka a Arewa
- Raji ya tambayi dalibansa su lissafa al’adu marasa ɗa'a ba su bin addini a jihar Kwara, inda suka lissafo su da dama
- Mutane da dama daga Ilorin sun fusata, suna cewa ya bata sunan garinsu, suna neman a kai shi kotu saboda zagin jama'a gaba ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Wani malamin Musulunci mai suna Dr Sharafdeen Gbadebo Raji ya ta da kura a jihar Kwara.
Malamin ya fuskanci suka sosai saboda ikirarin cewa ana bautar gumaka a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Asali: Facebook
Malami ya yi zargi kan bautar gumaka
Malamin wanda ya kammala digirin digirgir a fannin Shari’ar Musulunci daga Jami’ar Al-Madeenah a Saudiyya, ya ce akwai al’adun bautar gumaka a cikin birnin, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A wani taro da ya shirya don sukar wasu dabi’u da bai dace da Musulunci ba, Raji ya tambayi dalibai su lissafa fiye da hudu daga irin wadannan dabi’u da ake yi a Ilorin.
Ya ce:
“Sun ambaci wasu abubuwa da mutanen Ilorin ke yi da ke sabawa da Musulunci. Ku ƙara ambato wasu.”
Dalibin da ba a bayyana sunansa ba ya ce a Ilorin ana yin bautar gumaka, kuma suna yin bikin doya.
Raji ya bukaci karin bayani daga daliban, yana cewa irin wadannan dabi’un suna da yawa, kuma ya ba su kyauta bayan tattaunawar.
Wani dalibi ya ƙara da cewa:
“Suna zuwa Dutsen Sobi suna yin ibada a wurin. Mutane suna biyayya ga Alfas. Suna kai mata wurin Alfas don addu’a. Suna ibada a kaburbura.”

Asali: Original
Kalaman Sheikh sun jawo ce-ce-ku-ce
Sai dai wannan ikirari na Raji ya jawo cece-kuce daga ‘yan asalin garin Ilorin, inda da dama suka ce ya kamata a gurfanar da limamin a gaban kotu don batanci.
Wani malamin Musulunci daga Ilorin, Sheikh Labeeb Agbaji, ya yi gargaɗi ga Raji da ya daina zagin Ilorin.
Raji ya shahara wajen yada hudubarsa a TikTok, kuma an san shi da sukar wasu halayen da suka saba da Musulunci da ake yi a Najeriya.
Martanin masu amfani da kafofin sadarwa
Wasu mutane da dama masu amfani da kafofin sadarwa sun yi martani kan kalaman malamin inda suke sukarsa game da zargin da ya yi.
Wani mai amfani da TikTok mai suna Munir Aduagba ya ce:
“Abin bakin ciki ne ganin Musulmi yana zagin Ilorin da zargin bautar gumaka.
“Su bayyana ainihin gidajen da ake aikata hakan a cikin iyalansu, kada su ɗora laifi kan dukan Ilorin.”
Wani mai amfani da TikTok mai suna Layestewiy ya ce:
“Ilorin ba garin bautar gumaka bane, Alfa ba zai furta haka ba, na yi matukar bakin ciki da Dr Sharafdeen.
"Idan mutum ya zagi gari gaba daya da gangan, bai kamata a girmama shi ba har sai ya ba da hakuri."
Aljaoharry a shafin X ya ce:
“Babban matsalar Dr Sharaf shi ne yawan surutu da rashin tsari. Ya jagoranci yara su yi karya kan asalin garinsu.”
Wani mai amfani ya mayar da martani da cewa:
“…Ina tsanar abin da kuke yi, wallahi. Kun dauka Dr bai san Ilorin ba, malamansa daga Ilorin ne, kuma yana da masaniya.”
Malamin Musulunci ya rasu a Kwara
Mun ba ku labarin cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya nuna alhini kan rasuwar Muhammad Jamaalu Deen Yahyah Murtadoh Agodi.
Majiyoyi sun ce malamin ya rasu a safiyar Asabar, 29 ga Maris, 2025 wanda yake cikin zuriyar Sheikh Yahyah Agodi.
Gwamnan ya aike da ta’aziyya ga iyalansa da daukacin al’ummar Musulmi na masarautar Ilorin kan wannan babban rashi.
Asali: Legit.ng