Sojoji Sun Cafke Ɗan China a Samamen da Suka Kai Borno, An Ji abin da Ya Faru
- Dakarun soji sun kama wani ɗan ƙasar China a Borno yayin da suke gudanar da wani aikin hadin gwiwa na yaƙi da 'yan ta'adda a jihar
- An kama shi tare da wasu masu kai wa 'yan ta'adda kayayyaki da bayanai a Borno da Yobe, kwanaki kadan bayan kama wasu 'yan Pakistan
- Hedikwatar tsaro ta tabbatar da cewa an fara gudanar da cikakken bincike kan abin da ya kai ɗan Chinan yankin da sojoji ke aiki a lokacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – A ranar Juma'a, hedikwatar tsaro ta sanar da cewa an kama ɗan ƙasar China a yayin wani aikin yaƙi da ta'addanci da dakarun soji suka gudanar a jihar Borno.
Ko da yake ba a bayyana sunan sa ba, sojoji sun ce ɗan ƙasar Chinan, wanda ya yi ikirarin cewa ɗan hakar ma'adinai ne, a halin yanzu yana tsare kuma ana yi masa tambayoyi.

Asali: Twitter
Wannan ci gaban ya zo ne kasa da mako guda bayan da sojoji suka bayyana cewa sun kama wasu 'yan ƙasar Pakistan huɗu a yankin, a cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sojoji sun kama wani ɗan ƙasar China
A wancan lokacin, an zargi wadannan 'yan ƙasar wajen huɗu da hannu wajen horas da 'yan ta'adda da ke addabar yankin Arewa maso Gabas.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a, daraktan yaɗa labaran hedikwatar, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce an kuma kama wasu masu kai wa 'yan ta'adda kayayyaki.
"Dakarun soji sun kama mutum biyar da ke kai wa 'yan ta'adda kayayyaki, an kama masu ba 'yan ta'adda bayanai, da kuma wani ɗan ƙasar China wanda ya yi ikirarin cewa ɗan hakar ma'adinai ne.
"An kama mutanen ne a yayin gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a ƙananan hukumomin Kukawa da Ngala na jihar Borno, da kuma ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe tsakanin 5 zuwa 7 ga Yuni 2025."
"Me ya kai ɗan ƙasar China wurin?" - Kangye
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai mota, babur, wayoyin hannu, fasfo na ƙasar China, yayin da kuma aka kwato N10,000.00 daga hannunsu.
The Nation ta rahoto Janar Kangye ya yi mamaki kan abin da ya kai ɗan ƙasar Chinan wuraren da sojoji ke aikin yaki da ta'addanci yana mai cewa:
"Duk wanda aka kama, kamar yadda kuka san al'adar masu aikata laifuka, za su musanta hannu a zargin da ake yi masu. Amma tambayar ita ce: me ya kawo shi wurin a lokacin da ake kamen? Me ya kai shi yankin da sojojinmu ke gudanar da ayyuka?"
Janar Kangye ya tabbatar wa manema labarai cewa ana gudanar da cikakken bincike don tantance manufar wanda ake zargin da kuma yiwuwar haɗinsa da ƙungiyoyin 'yan tawaye.

Asali: Twitter
Sojoji sun karyata zargin kin kai dauki da wuri
Ya ƙara da cewa:
"An tsare ɗan ƙasar China kuma ana masa tambayoyi. Da zarar an kammala binciken, za mu sanar da jama'a cikakkun bayanai, game da dalilin da ya sa je wurin, yadda aka kama shi, da kuma ko yana da abokan aiki."
Ya kuma yi watsi da zargin cewa dakarun sojoji sukan jinkirta wajen amsa kiran gaggawa a lokacin hare-hare, musamman a yankunan karkara.
"Wani lokaci, ana kai hari kilomita 10 zuwa 15 daga sansanin soji mafi kusa. Kafin a tura sojoji, dole ne a gano rukunin da ya dace, a naɗa kwamanda, kuma a samu motoci da kayayyaki. Duk wannan yana ɗaukar lokaci."
- Janar Kangye.
Sojoji sun kashe hatsabiban 'yan bindiga 16
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar da cewa sojoji sun kashe shahararrun jagororin 'yan bindiga shida da wasu mayaƙa goma a Jihar Zamfara.
DHQ ta bayyana sunayen manyan 'yan bindigar da aka kashe da suka haɗa da Auta, Abdul Jamilu, Salisu, Babayé, da kuma ɗan Ado Alieru.
Wannan farmakin, a cewar Hedikwatar Tsaron, ya nuna jajircewar sojoji wajen ragargazar 'yan ta'adda tare da dawo da zaman lafiya a jihar.
Asali: Legit.ng