June 12: Ɗan Abiola Ya Faɗi Abin da IBB Ya Faɗa Musu a Asirce kan Soke Zaɓen
- Dan marigayi MKO Abiola ya bayyana abin da tsohon shugaban soja, Janar Ibrahim Babangida, ya yi asirce kan soke zaben 1993
- A cewar Lekan Abiola, IBB ya taba tura wakili a kowace ranar 12 ga Yuni, yanzu kuma ya fito fili ya amsa laifinsa.
- Ya ce furucin IBB ya tabbatar da cewa MKO Abiola ya lashe zaben 1993, ya kawo karshen shakku da cece-kuce kan sakamakon
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Dan marigayi MKO Abiola ya yi magana kan Janar Ibrahim Badamasi Babangida game da soke zaben 1993.
Lekan Abiola ya bayyana cewa tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya nemi gafara daga iyalansu kan soke zaben mai tarihi.

Asali: Getty Images
Abin da IBB ya fadawa Iyalan Abiola
Lekan ya bayyana hakan ne yayin taron tunawa da MKO Abiola da kuma shirin ƙaddamar da littafi mai taken “MKO Abiola: Symbol of Democracy”, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Yayin da yake magana da ’yan jarida a taron, Lekan ya ce dangin sun ji annashuwa ganin yadda Babangida ya fito fili ya amince da kuskurensa tare da neman gafara.
Ya ce:
“Mun dawo daga Amurka, mun gana da IBB, ya nemi gafara a asirce. Lokacin da ya fito fili ya ce abin da ya aikata kuskure ne, da cewa MKO ne ya ci zabe, ya maimaita abin da ya ce a sirrance.
"Duk shekara, sai ya aiko da wani domin wakiltarsa a ranar 12 ga Yuni.”

Asali: Twitter
Lekan Abiola ya yabi IBB kan fadin gaskiya
Lekan ya kuma jaddada muhimmancin wannan nadama a fili, yana cewa ya kamata tuni a yi hakan tun da dadewa.
“Tun da farko, wannan neman afuwa ta sirri ba ta da wani tasiri sosai. Kamar wanda ya buge ka a fili amma ya ce kayi hakuri a ɓoye.”
- Cewar Lekan
Ya ƙara da cewa amincewar Babangida a bainar jama’a ya taimaka wajen tabbatar da gaskiyar nasarar MKO Abiola, ya kawo ƙarshen shakku da muhawara da aka dade ana yi.
Ya kara da cewa:
“Yadda ya fito ya ce MKO ya ci zabe ya sa muke cikin kwanciyar hankali. Wasu suna cewa ko MKO ya ci zaben kuwa? Amma yanzu ya fitar da sakamakon.
"A hukumance, an tabbatar da nasararsa, kuma babu cece-kuce a kai.”
Majiyoyi sun ce ’ya’yan marigayi Abiola sun roki Tinubu da ya sanya hannu a dokar da za ta tabbatar da ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya ta doka wanda ba za a soke daga baya ba.
Hamza Al-Mustapha ya magantu bayan mutuwar Abacha
A baya, kun ji cewa Manjo Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewa mutuwar Janar Sani Abacha da MKO Abiola ta faru ne ta hanyar iri ɗaya.
Al-Mustapha ya ce batun soke zaɓen 12 ga Yuni 1993 ya fi yadda mutane ke fahimta girma.
Tsohon dogarin Abacha ya kuma nesanta kansa daga zargin da Janar Ibrahim Babangida ya yi wa Abacha a littafinsa game da rushe zaɓen 1993 da aka ce Abiola ya lashe.
Asali: Legit.ng