Shugaba Tinubu Ya Taɓo Buhari a Jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya a gaban Majalisa
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tuna da Muhammadu Buhari a jawabinsa na ranar dimokuradiyya a zauren Majalisar Tarayya
- Mai girma Tinubu ya yabawa Buhari bisa matakin da ya ɗauka na ayyana 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyyar Najeriya
- Bola Tinubu ya sha alwashin cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen kare tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabi magabacinsa, Muhammadu Buhari bisa ayyana ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Tinubu ya ce wannan abin alheri da tsohon shugaban kasa Buhari ya yi, ya gyara zaluncin da aka yi a baya, kuma ya girmama muradan ƴan Najeriya.

Asali: Facebook
Tinubu ya kwararo yabo ga Buhari ne a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya wanda ya gabatar a zaman haɗin guiwa na Majalisun Tarayya, Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Abin da Bola Tinubu ya faɗa kan Buhari
"Dole na jinjinawa magabacina, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya koma baya domin gyara wani babban kuskure ta hanyar ayyana ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya."
Ya kuma jaddada cewa Buhari ya amince da Cif M.K.O. Abiola da abokin takararsa Babagana Kingibe a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993.
A cewarsa, galibin ’yan ƙasa sun ɗauki wannan zaɓe da Abiola ya lashe a matsayin zaɓe mafi inganci da gaskiya a tarihin Najeriya, amma gwamnatin sojoji ta soke shi.
Tinubu ya tuna gwagwarmayar da suka yi
Shugaba Tinubu na ɗaya daga cikin waɗanda suka taka gagarumar rawa a gwagwarmayar dawo da mulkin farar hula a shekarun baya.
Ya bayyana wannan lokaci a matsayin mai taɓa zuciya da kuma tuna sadaukarwar waɗanda suka ba da rayukansu domin ganin an dawo da dimokuraɗiyya.
"Lokacin da na shigo cikin wannan zauren mai daraja, na cika da jin daɗin abin da muka cimma da kuma ƙudurinmu na ci gaba da ƙarfafa tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Asali: Facebook
"Zan kare dimokuradiyya" - Bola Tinubu
Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa tun daga 2018, Najeriya ke bikin Ranar Dimokuraɗiyya a ranar 12 ga Yuni domin girmama waɗanda suka yi sadaukarwa don ganin an dawo da gwamnatin talakawa.
A rahoton Channels tv, Tinubu ya ci gaba da cewa:
“A yau, ina tabbatar maku da cewa zan yi duk mai yiwuwa don gina da kare dimokuraɗiyyar ƙasar nan, kamar yadda Allah Ya ƙaddara.”
Bola Tinubu ya raba lambobin yabo
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Ƙasa Tinubu ya ba marigayiya Kudirat Abiola, Shehu Musa Yar’Adua da Humphrey Nwosu lambar yabo ta ƙasa.
Tinubu ya bai wa waɗannan mutane lambar yabo ta ƙasa ne bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta zauna da kafarta a Najeriya.
Sauran waɗanda shugaban kasar ya karrama a yau Alhamis, 12 ga watan Yuni, 2025 sun haɗa da Marigayi Bola Ige, Balarabe Musa, Alfred Rewane, Frank Kokori da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng