Sufetan Ɗan Sanda Ya Sha da Ƙyar a Hannun Matasa kan Zargin Satar Wayoyin Lantarki
- Rundunar ‘yan sandan Benue ta kama wani Sufetan da wasu biyu da ake zargin sun saci wayoyin lantarki a garin Makurdi
- An kama su ne bayan sun shiga wani shago a unguwar Ankpa da ke Makurdi inda mutanen gari suka fara jibgarsu kafin ‘yan sanda su iso
- Sufeta Ishaku ya jikkata sosai, yanzu yana hannun ‘yan sanda, zai fuskanci hukunci bayan an tabbatar da sabawa doka da oda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da cafke wani Sufetan dan sanda kan zargin sata a birnin Makurdi.
Rundunar yan sanda ta ce an cafke shi ne da wasu mutane biyu da ake zargi da satar wayoyin lantarki a birnin Makurdi da ke jihar Benue.

Asali: Facebook
Wata majiya daga rundunar ta shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Yuni, misalin karfe 8 na safe a Makurdi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Dalilai da ke sanya mutane satar wayar lantarki
Satar manyan wayoyin lantarki ya zama ruwan dare a Najeriya inda gwamnati, kamfanoni da al'umma ke tafka asara kan sace-sacen da ake yi.
Mafi yawan masu barayin suna mutuwa a kokarin satar wayar saboda dawowar wutar lantarki wanda ke rike su har su mutu.
Wasu sun tabbatar da cewa ana sayan wayoyin ne da makudan kudi wanda hakan ne ya kan sanya wasu sayar da ransu domin samun wannan kudi.
Yadda mutane suka balle shago a Benue
An bayyana cewa mutum uku sun balle wani shago dake bayan gidan Alhaji Dash a Ankpa, inda suka sace wayoyin lantarki da mutane ke amfana dasu domin samun wuta a yau da kullum.
“Tun kafin ‘yan sanda su iso, mutane sun riga sun afka musu da niyyar kashe su."
- Cewar sanarwar rundunar ‘yan sanda

Asali: Original
Yan sanda sun kai dauki domin ceto su
‘Yan sanda daga ofishin ‘D’ sun garzaya wurin cikin gaggawa inda suka ceci wadanda ake zargi, wato Mohammed Umaru, Mohammad Mutala da Sufeta Innocent Ishaku.
Sufetan dan sanda, Ishaku ya samu munanan raunuka sakamakon dukan da aka masa, daga bisani aka kai shi asibitin ‘yan sanda a Makurdi.
Bayan ya samu sauki, an sallame shi daga asibitin, bincike ya nuna cewa an mayar da shi rundunar Kaduna watanni shida da suka gabata.
“Yanzu haka yana tsare, an bayyana shi da laifi, kuma yana jiran hukuncin zaman dakin hukuncin ‘yan sanda."
- Cewar majiyar.
Matasa sun hallaka sufetan ɗan sanda a Plateau
Mun ba ku labarin cewa rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar wani jami'inta mai muƙamin sufeta da aka kai wa farmaki a Jos da ke jihar Plateau.
Rahotanni sun ce an farmaki dan sandan ne mai suna Ikale Muhammed a ranar 1 ga Maris din 2025 yayin da yake kokarin kama wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.
Wanda ake zargin ya tsere, amma daga baya ya dawo da ‘yan acaba suka kai wa ‘yan sanda hari inda Muhammed ya samu munanan raunuka wanda daga bisani aka tabbatar da cewa ya mutu.
Asali: Legit.ng