Fitattun Ƴan TikTok 3 Sun Shiga Matsala kan Wallafa Hotunan 'Batsa' a Jihar Kano

Fitattun Ƴan TikTok 3 Sun Shiga Matsala kan Wallafa Hotunan 'Batsa' a Jihar Kano

  • Wasu fitattun ƴan TikTok uku a jihar Kano sun fara shiga matsala sakamakon wallafa hotuna da bidiyon rashin ɗa'a
  • Wata kotu a Kano ta kama ƴan TikTok ɗin da laifin haɗa baki wajen aikata laifi da yaɗa hotuna batsa marasa kyawun gani
  • Mai Shari'a Halima Wali ta yanke masu hukunci ɗauri a gidan yari na tsawon shekara ɗaya da wata guda ko su biya tara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wata Kotun Majistare da ke zama a Norman’s Land a cikin birnin Kano, ta kama fitattun ƴan TikTok uku da laifin yaɗa hotuna da bidiyon rashin ɗa'a.

Kotu ta yanke wa fitattun masu amfani kafafen sada zumunta uku, hukuncin daurin shekara guda da wata daya kowannensu, saboda wallafa hotunan rashin kunya a manhajar TikTok.

TikTik ya jawo wa wasu mutum 3 ɗauri a Kano.
Kotu a Kano ta ɗaure ƴan TikTok 3 a gidan yari kan yaɗa hotunan batsa Hoto: Getty Image
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Sumayya Muhammad, Usman Majidadi da Usman Ibrahim Kalar Kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yadda aka gurfanar da ƴan TikTok a kotu

Tun farko dai hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ce ta gurfanar da su gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda uku kaɗai.

Tuhume-tuhumen da hukumar ta shigar a kansu sun haɗa da, haɗa baki wajen aikata laifi, wallafa abin da bai dace ba a kafar sada zumunta da wallafa hotuna da ke iya gurbata tarbiyya da dabi’un jama’a.

Duka ƴan TikTok uku da aka gurfanar a gaban kotu, sun amsa laifinsu cikin sauƙi ba tare da wahal da kansu da alkali ba.

Bayan kammala sauraron kowane ɓangare, kotun ta ɗaure waɗanda ake tuhuma na tsawon shekara ɗaya da wata guda ko zaɓin biyan tara, rahoton Linda Ikeji Blog.

Hukuncin da kotu ta yi kan kowace tuhuma

Alkalin kotun, Halima Wali, ta yanke musu hukunci kamar haka:

  • Kowane daga cikinsu zai yi watanni hudu a gidan yari ko zaɓin tara ta Naira 50,000 saboda laifin haɗa baki wajen aikata laifi
  • Ɗaurin watanni shida kan kowane daga cikinsu ko ya biya tara ta Naira 50,000 saboda wallafa hotuna rashin kunya.
  • A ƙarshe, kowane daga cikin waɗanda suka aikata laifin zai shafe watanni uku ko zaɓin tara ta N70,000 saboda bata lokacin masu gabatar da kara.
Kotu ta hukunta yan TikTok 3 a Kano
Kotu ta yanke wa ƴan TikTok 3 hukunci a laifuffuka 3 Hoto: @ImranmuhdX
Asali: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa kotun ta ba ƴan TikTok din zaɓi, ko dai su biya tarar laifuffukan ɗaya bayan ɗaya, ko kuma a ɗaure su na shekara guda da wata ɗaya.

Aikin Hisbah wajen gyaran tarbiyya

Arewacin Najeriya na ɗaya daga cikin yankunan da ke da al’ada da tarbiyya mai kyau bisa tushen addinin Musulunci.

Domin kare waɗannan dabi’u da tabbatar da tsaftar rayuwa, an kafa Hukumar Hisbah a jihohi da dama, musamman Kano, domin sanya ido da ɗaukar mataki a kan abubuwan da ke karya tarbiyyar al’umma, musamman tsakanin matasa.

Hisbah na taka rawa wajen dakile yaɗuwar batsa, rashin ɗa’a a kafafen sada zumunta, shaye-shaye da cin zarafin al’umma.

A lokuta da dama, hukumar na shiga cikin lamarin da ke danganta da rigingimu na ɗabi’a, inda take kai farmaki ko tsare masu aikata laifin da ya sabawa koyarwar addini ko dokokin jihar.

A cikin irin wannan yunƙuri ne, hukumar ta shiga cikin lamarin waɗanda aka yankewa hukunci a kotun Kano, bayan da suka wallafa bidiyo da hotuna na rashin ɗa’a a TikTok.

Hisbah na ganin cewa irin waɗannan abubuwa na da tasiri mara kyau ga tarbiyyar matasa, don haka take amfani da hanyoyi na ilimantarwa da kuma ladabtarwa don rage faruwar su.

Duk da ce-ce-ku-cen da ake yawan samu, Hisbah na ganin aikinta a matsayin garkuwa ga al’umma daga lalacewar dabi’u da gurɓacewar zamantakewa.

Kotu ta hukunta ƴan TikTok a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu a Legas ta yanke wa yan TikTok biyu hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan gyaran hali saboda wulaƙanta Naira.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa watau EFCC ta kama waɗanda ake zargin kuma ta gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.

Mai shari'a Owoeye ya yanke wa kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhumar hukuncin ɗaurin watanni shida tare da zaɓin biyan tarar N200,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »