"An Yi Ta'asa": Mahara Sun Sake Tafka Barna a Jihar Plateau
- An ƙona tarin wasu gidaje a ƙauyen Gyenbwas da ke yankin Langai a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau
- Mutanen yankin sun nuna yatsa ga ƙabilar Berom kan kai harin da aka ƙona gidaje 96 tare da sace kayan abinci, katifu shanu da sauran kayayyaki
- Sai dai, 'yan ƙabilar Berom sun musanta zargin, inda suka bayyana cewa su ma ba su tsira ba daga hare-haren ƴan ta'adda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - An ƙona gidaje 96 ƙurmus a ƙauyen Gyenbwas, da ke yankin Langai, ƙaramar hukumar Mangu a jihar Plateau.
Mazauna yankin sun zargi masu kai harin da sace abinci, katifu, shanu da wasu kayan amfani masu daraja.

Asali: Facebook
Madugun Langai, Alhaji Yakubu Umar, ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Talata lokacin da aka yi hira da shi a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Mahara sun ƙona gidaje a Plateau
A cewarsa, ban da mutane biyu da aka kashe a ranar Litinin, an sake gano wata gawar mutum guda a ranar Talata, wanda hakan ya kai adadin waɗanda suka mutu zuwa uku.
Al’ummar yankin sun zargi Berom da kai harin, amma 'yan ƙabilar sun musanta hakan.
“Ba mu taɓa fuskantar irin wannan ta’asa ba. Waɗanda suka kai harin sun ƙone kayan aiki, tufafi, kayan abinci da sauran kayayyaki."
"Sun kuma sace kayan da kudinsu ya kai miliyoyin naira. Muna zaune lafiya da kowa, shi yasa muka yi mamakin abin da ya faru."
- Alhaji Yakubu Umar
An buƙaci gwamnatin Plateau ta kawo ɗauki
Basaraken ya buƙaci gwamnatin jihar da kuma ta ƙaramar hukumar Mangu da su binciko waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika su hukunta su yadda ya kamata.
Haka kuma, ya roƙi gwamnatin jihar da ta tallafa wa waɗanda suka rasa dukiyoyinsu a harin.
Ƴan ƙabilar Berom sun musanta kai harin
A gefe guda, shugabancin ƙungiyar matasan Berom (BYM) ta musanta zargin da aka yi musu na kai harin, inda suka bayyana hakan a matsayin ƙarya ce.
Shugaban ƙungiyar BYM, Dalyop Solomon, wanda ya musanta zargin, ya bayyana cewa
“Jiya, wasu mambobinmu guda uku da suka je gona a yankin sun gamu da harin ƴan ta’adda kuma yanzu haka suna kwance a asibiti."
"Abin da muka sani shi ne mutanenmu suna fuskantar hare-hare. Fulani na ƙirƙiro ƙaryar ne don su kare irin ta’asar da suke aikatawa."
Mahara sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun mahara ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Maharan sun hallaƙa aƙalla mutane bakwai a wani sabon harin da suka kai a ƙauyen Mushere da ke cikin ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
Mummunan harin ya auku ne sakamakon yunƙurin sace wani mutum da kisan wani fasto da kuma wani hari da aka kai wa wata rugar Fulani a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng