Rashin Tsaro: Sojoji Sun Kama 'Dan China da Ya Shigo Borno Hakar Ma'adanai

Rashin Tsaro: Sojoji Sun Kama 'Dan China da Ya Shigo Borno Hakar Ma'adanai

  • Hukumomin tsaro sun karyata rade-radin da ke cewa an kama wani dan kasar China da hannu a ayyukan Boko Haram a Gamboru, Jihar Borno
  • An bayyana cewa mutumin mai hakar ma’adanai ne da aka kama yayin da yake ƙoƙarin barin yankin da sojoji ke aiki ba tare da izini ba
  • Rahoto ya nuna an mika shi ga hukumar DSS domin yi masa cikakken bincike, inda hukumomi suka tabbatar ba shi da alaƙa da ‘yan ta’addan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Wasu rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa an kama wani dan China a Gamboru, Jihar Borno, bisa zargin yana da hannu a ayyukan Boko Haram.

Amma daga bisani rahoto ya bayyana cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne, kuma hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa mutumin ba shi da wata alaka da Boko Haram.

Dan China da aka kama ya ce daga Chadi ya fito
An kama dan China a Borno kan zargin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba. Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan yadda ake cigaba da binciken mutumin a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A cewar majiya daga jami’an tsaro, wanda aka kama ɗin mai hakar ma’adinai ne da aka tsare bisa laifin barin yankin da dakarun soji ke aiki ba tare da izini ko wani bayani ba.

'Dan Chinan ba shi da alaka da Boko Haram

Rahoton ya bayyana cewa an kama mutumin ne yayin da yake ƙoƙarin fita daga yankin da sojoji ke sintiri ba tare da izini daga hukumomin tsaro ba, wanda hakan ya tada musu hankali.

Wata majiyar jami'an tsaro ta ce:

“Ba shi da alaƙa da Boko Haram. Mun kama shi ne kawai saboda ya ƙi bin ka’ida wajen barin yankin sojoji. Mun mika shi ga DSS domin yi masa bincike,”

An kuma bayyana cewa mutumin ya fito ne daga kasar Chadi, kuma yana gudanar da aikin hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a cikin yankin Gamboru.

Gwamnatin Borno ta haramta hako ma’adanai

Tun cikin shekarar 2023 ne gwamnatin jihar Borno ta haramta dukkan nau’ukan hakar ma’adinai a fadin jihar, domin dakile matsalolin tsaro da barnar muhalli.

Duk da wannan doka da Majalisar Dokokin jihar ta amince da ita, har yanzu ana samun wasu mutane da ke gudanar da ayyukan hako ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a sassa daban-daban na jihar.

Zulum ya hana hako ma'adananai a Borno
Gwamnatin Borno ta sha alwashin hukunta masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Twitter

Hukumomi sun sha alwashin dakile wannan matsala, musamman ganin cewa tana iya zama wata kafa da masu aikata laifuffuka ke amfani da ita wajen kutsawa kai cikin ƙasar nan.

Rahoton ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar cewa mutumin da aka kama yana da alaƙa da Boko Haram, tare da cewa irin waɗannan rade-radin na iya jefa jama’a cikin rudani.

Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki kan wasu 'yan Boko Haram a jihar Borno.

Harin ya jawo kashe 'yan Boko Haram da dama tare da kwato da yawa daga cikin makaman da suke kai hari da su.

Legit ta rahoto cewa sojoji sun farmaki Boko Haram din ne yayin da suke kokarin kai hari yayin bikin babbar sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »