Aminu Ado Bayero Ya Ɗaga Darajar Alan Waƙa daga Sarautarsa Ta Ɗan Amanan Bichi

Aminu Ado Bayero Ya Ɗaga Darajar Alan Waƙa daga Sarautarsa Ta Ɗan Amanan Bichi

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya daga darajar mawaki Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) daga Ɗan Amanan Bichi
  • Baffa Babba Dan'agundi ne ya bayyana hakan cikin wani bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a Facebook ranar Lahadi, 8 ga Yunin 2025
  • Dan'agundi ya ce bayan shawarwari daga manyan mutane a Najeriya, Sarki ya yanke shawarar kara darajar Alan Waƙa zuwa Ɗan Amanan Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya daga darajar Aminu Ladan Abubakar game da sarautar da ya ba shi a baya.

Basaraken ya karawa mawakin da aka fi sani da Alan Waƙa girma daga muƙaminsa na Ɗan Amanan Bichi.

Aminu Ado ya inganta sarautar Alan Waƙa
Aminu Ado Bayero ya daga darajar sarautar Alan Waƙa. Hoto: Masarautar Kano, Aminu Ladan Abubakar.
Asali: Facebook

Aminu Ado ya inganta sarautar Alan Waƙa

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin Masarautar Kano ya wallafa a Facebook a yau Lahadi 8 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

A cikin bidiyon, an gano Aminu Babba Dan'agundi yana shelanta cewa Alan Waƙa ya zama Ɗan Amanan Kano daga yanzu.

Dan'agundi ya ce lokacin da Aminu Ado ke sarautar Bichi, ya ba Alan Waƙa Ɗan Amanan Bichi.

Dalilin ƙarawa Alan Waƙa girman sarauta a Kano

Amma yanzu bayan shawarwari daga manyan mutane a fadin Najeriya, ya daga darajarsa zuwa Ɗan Amanan Kano.

Dan'agundi ya ce:

"Auzubillahi minasshaidanir rajim, bismillahir rahmanir rahim, godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW).
"Jama'a Assalamu Alaikum, Mai Martaba, Sarkin Kano ya umarce ni da na sanar da Ala Sarkin Waka ya sani cewa lokacin da yake Sarkin Bichi ya ta ba shi sarautar Ɗan Amanan Bichi.
"Yanzu ya samu shawarwari daga muhimman mutane a wannan kasa ta mu, don haka ya daga sarautar da ya ba ka daga Ɗan Amanan Bichi zuwa Ɗan Amanan Kano.

"Don haka sai a duba rana wacce ta dace wanda za a zo a yi bikin nada ka sarautar."
Aminu Ado ya daga darajar sarautar Alan Waƙa
Aminu Ado ya ƙarawa Alan Waƙa girman sarauta a Kano. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: UGC

Alan Waƙa ya godewa Aminu Ado Bayero

A bangarensa, Ɗan Amanan Kano, Aminu Ladan Abubakar ya yi godiya ta musamman ga basaraken bisa wannan karamci da ya nuna masa.

Alan Waƙa ya yi godiya a yau Lahadi 8 ga watan Yunin 2025 a shafinsa na Facebook wanda ya nuna matukar farin cikinsa.

Mawakin ya ce ba zai taba mantawa da karamcin da Sarki ke yi masa ba da kuma dattakun da yake nuna wa inda ya ce al'umma suna yabonsa.

Aminu Ado ya fitar da jadawalin bukukuwan sallah

Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Idi da karɓar gaisuwar Sallah na tsawon kwanaki.

Wannan na kunshe a cikin wani jadawali da aka fitar bayan Aminu Ado Bayero ya goyi bayan haramta hawan Sallah.

A cikin kwanaki hudu da za a shafe kwanaki biyar ana gudanarwa, babu inda aka nuna Basaraken zai yi hawa ko zai bar fadarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »