'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sace Malamin Addini da Wasu Matafiya a Borno

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sace Malamin Addini da Wasu Matafiya a Borno

  • Ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun yi ta'asa a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wani limamin cocin Katolika
  • Tsagerun ba su tsaya iya nan ba, sai da suka yi awon gaba da wasu matafiya bayan sun tare motocinsu a kan hanya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta’addan Boko Haram/ISWAP sun sace wani limamin cocin Katolika, Rabaran Daniel Afina a jihar Borno.

Ƴan ta'addan na Boko Haram sun sace malamin addinin ne tare da wasu mutane tara bayan sun kashe mutum guda a kan hanyar Gwoza-Limankara da ke jihar Borno.

'Yan ta'addan Boko Haram sun yi barna a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun sace malamin addini a Borno Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana hakan jiya cikin garin Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ƴan Boko Haram sun yi aika-aika a Borno

Majiyar ta bayyana cewa Rabaran Afina, wanda shi ne mai kula da ayyuka a wata ƙungiyar agaji ta Kiristoci mai zaman kanta, yana dawowa daga Mubi ne tare da wasu ma’aikatan ƙungiyar guda biyu a cikin mota lokacin da ƴan ta’addan suka kai musu kwanton-bauna a kan hanyar Gwoza-Limankara.

A cikin wannan hari, ƴan ta’addan sun bindige ɗaya daga cikin ma’aikatan ƙungiyar har lahira, sannan suka kama Rabaran Afina, yayin da wasu daga cikin su suka samu damar tserewa.

Har ila yau, majiyar ta ce wasu matafiya tara da ke cikin wata mota daban da ta limamin suma an kama su a lokacin harin, saboda an yi kwanton ɓaunar ne a lokaci guda ga motar limamin da sauran matafiya.

Ma’aikacin da ya tsira daga harin ya koma Maiduguri don sanar da hukumomi da iyalai game da faruwar lamarin.

Majiyar ta ƙara da cewa bayan an sace Rabaran Afina, ƴan ta’addan sun tuntuɓi iyalan limamin ta wayar salula, inda suka bar shi ya yi magana da su domin tabbatar da cewa an sace shi.

Sai dai har zuwa lokacin da suka kira, ba su nemi kuɗin fansa ba.

An tabbatar da sace malamin addini a Borno

Wani babban jami’i a ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Borno ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu rahoton sace limamin tare da kisan ma’aikacinsa.

'Yan ta'addan Boko Haram sun sace malami a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun yi barna a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’in ya roƙi gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su hanzarta ɗaukar matakai domin kubutar da limamin da sauran mutanen da aka sace.

Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta ƙara ƙaimi da jajircewa wajen kare rayukan ƴan ƙasa musamman a yankunan da ake fama da hare-haren ƴan ta’adda.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare suna barazana ga ƴancin walwala da addini, don haka ya kamata hukumomi su ɗauki alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Zulum ya ba sojoji tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba da kuɗaɗe domin iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a fagen daga.

Gwamna Zulum ya ba da N100m domin a raba ga iyalan sojojin da suka rasu da kuma waɗanda suka samu raunuka.

Ya kuma yaba da irin jajircewa da sadaukarwar da sojojin suke yi wajen tabbatar da an samu zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »