Babbar Sallah: Dillalan Mai Sun Sake Rage Farashin Fetur domin Sauƙaƙawa Jama'a

Babbar Sallah: Dillalan Mai Sun Sake Rage Farashin Fetur domin Sauƙaƙawa Jama'a

  • ’Yan kasuwar man fetur a Najeriya sun rage farashin lita don jawo hankalin masu saya da ƙara gasa a kasuwar hada-hadar mai
  • A Abuja, kamfanonin man fetur irin su AA Rano da Shafa sun sauke farashin lita daga ₦910 zuwa ₦900 a mafi yawan gidajen mai mallakinsu
  • Chinedu Ukadike ya bayyana cewa yanzu kasuwa ce ke tsara farashi, ba gwamnati ba, saboda ’yancin kasuwancin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - ’Yan kasuwar man fetur a Najeriya sun rage farashin man fetur domin jawo hankalin masu saye da kuma duba zuwa ga bukukuwan sallah da ake yi.

Wannan matakin ya biyo bayan ƙalubalen da kasuwar man fetur ke fuskanta kan gasa daga kamfanoni da dama a sassan ƙasar duba da halin da ake ciki.

An sake farashin fetur a Najeriya
Dillalan mai sun duba halin da ake ciki kan tsadar mai. Hoto: NNPC Limited.
Asali: Facebook

Yadda kamfanonin mai suka rage farashin fetur

Rahoton Legit ya bayyana cewa wasu gidajen man Abuja sun rage farashin man da akalla N10 domin jan hankalin abokan ciniki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Wannan mataki ya zo a daidai lokacin da ake bukukuwan sallah yayin da yan kasar ke fama da tsadar rayuwa sanadin cire tallafin mai da daukar wasu matakai da aka yi.

Kamfanonin man fetur kamar Ranoil, Shafa, da AA Rano sun fara sayar da lita ɗaya na man fetur a kan farashin ₦900 maimakon tsohon farashin ₦910.

Abin da kakakin kungiyar dillalan mai ta ce

Mai magana da yawun kungiyar masu zaman kansu ta dillalan man fetur, Chinedu Ukadike, ya ce wannan sauyi alamar cigaban ’yancin kasuwa ne.

Ya bayyana cewa gwamnati ba ta ƙara tsoma baki a tsara farashin man fetur ba, yanzu kasuwa ce ke ƙayyade farashin bisa buƙata da wadata.

Ukadike ya kuma bayyana a baya cewa farashin lita ɗaya na man fetur na iya faɗuwa har zuwa ₦800 idan abubuwa suka daidaita, cewar Daily Post.

Ya ce wannan mataki zai kara sanya gasa a hada-hadar kasuwancin mai wanda zai sake kawo daidaito da sauki a tsakanin yan kasuwa.

Yan kasuwa sun rage farashin man fetur
Dillalan mai sun rage farashin fetur ana bikin sallah. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Nawa kamfanonin MRS, AP ke siyar da lita?

Kamfanonin man fetur kamar MRS, AP Ardova, da Bovas suna sayar da lita tsakanin ₦875 zuwa ₦895 a Abuja da Lagos.

Matatar Dangote da NNPCL suna iya rage farashin man fetur bayan bikin Sallah don su ci gaba da jan hankalin masu saya.

Wannan matakin yana ƙara tabbatar da cewa 'yancin kasuwa yana da tasiri wajen sauya farashin kaya a Najeriya.

Legit Hausa ta tattauna da mai jigilar mai

Muhammad Ahmad Anwar ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa ba za a ce ba a samu ragi ba amma dai bai kai ya kawo ba.

Ya ce:

"Komai kankantar ragi yana da amfani amma gwara a yi ragin da kowa zai tabbatar madadin irin wannan tsarin da bai wuce ragin N10 ba."

Ya shawarci hukumomi da su duba halin da ake ciki na tsadar mai wanda ya kara farashin kaya.

Dangote ya sake rage farashin man fetur

Mun ba ku labarin cewa duk da cewa Matatar Dangote ta saukar da farashin mai tsakanin ₦875 da ₦905, gidajen mai sun ki sauya farashin da suke sayar da man.

Matatar Dangote ta rage farashin har sau shida a 2025, amma ana ci gaba da sayar da mai tsakanin ₦890 zuwa ₦910 a gidajen mai da ke fadin kasar baki daya.

Masu gidajen mai sun koka da saukar farashi ba tare da sanarwa ba, inda suka ce hakan yana jawo masu asarar mai da rashin riba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »