Tsohon Mawakin Gargajiya a Najeriya Ya Rasu, Atiku da Gwamna Mbah Sun Yi Ta'aziyya

Tsohon Mawakin Gargajiya a Najeriya Ya Rasu, Atiku da Gwamna Mbah Sun Yi Ta'aziyya

  • Rahoto ya nuna cewa shahararren mawakin gargajiya Mike Ejeagha, ya rasu bayan fama da doguwar rashin lafiya a jihar Enugu
  • Ejeagha ya kasance gwarzon raya al’ada da hikimomin Igbo, musamman ta hanyar wakokinsa da ke ɗauke da darussa
  • Gwamna Peter Mbah da Atiku Abubakar sun bayyana alhini da kudurin tunawa da irin gudummawar da ya bayar a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Shahararren mawaki kuma gwarzon raya al’ada daga yankin Kudu maso Gabas, Mike Ejeagha, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 95.

Mawakin ya rasu ne da yammacin ranar Juma’a a asibitin 32 Garrison da ke Enugu bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Mawakin gargajiya ya rasu a Najeriya
Mawakin Najeriya a jihar Enugu ya rasu. Hoto: @AfamDeluxo
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya tabbatar da rasuwar mawakin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

'Dan marigayin, Emma Ejeagha ya tabbatar da rasuwar a wata hira da manema labarai, yana mai bayyana cewa mahaifinsa ya kasance gwarzon da ya rayu cikin koyi da al’adar gargajiya.

Ejeagha ya shahara da wakokin da ke ɗauke da darussa, karin magana da hikimomi na Igbo, wanda hakan ya sa ya zama fitaccen mai rera labarai ta hanyar kiɗa a Najeriya.

Rayuwa da tasirin wakokin Mike Ejeagha

Punch ta wallafa cewa an haifi Mike Ejeagha a ranar 4 ga Afrilu, 1930, kuma ya fara sana’ar waka tun a shekarun 1950.

Ya shahara sosai a shekarun 1970 lokacin da ya rika gabatar da shirin "Akuko N’ Egwu" a tashar NTA, shirin da ke haɗa waka da labaran al’adu.

Daya daga cikin wakokinsa mafi shahara, “Gwogwogwo,” ta sake samun karɓuwa a shekarar 2024 bayan wani sabon fasalin wakar da ɗan wasan barkwanci Brian Potter ya fitar.

Bincike ya tabbatar da cewa hakan ya jawo hankalin matasa da ba su san Ejeagha ba a baya zuwa ga fasahar wakokinsa.

Peter Mbah ya yi jajen mutuwar wamakin Najeriya
Gwamna Peter Mbah ya yi jajen mutuwar wamakin Najeriya. Hoto: @PNMbah
Asali: Twitter

Wakokinsa sun kasance cike da nasiha, dariya da ilimi, wannan ya ba shi damar samun mabiya da dama a tsakanin manya da matasa, musamman a yankin Kudu maso Gabas.

Gwamna Mbah da Atiku sun yi ta'aziyya

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana alhini bisa rasuwar Ejeagha, yana mai bayyana shi a matsayin zakaran raya al’adun gargajiya.

Peter Mbah ya ce:

“Ejeagha ya dauki hikimomin ƙauyuka ya mayar da su waka mai jan hankali, wacce ke da ma’ana ga duk al’ummomi.”

Gwamnan ya sha alwashin tunawa da marigayin ta hanyar ɗaukar matakan da za su daɗe suna tuna irin gudummawar da ya bayar ga al’adar Enugu da Najeriya baki ɗaya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya wallafa sakon ta’aziyya a X yana cewa Najeriya ta yi babban rashi.

Tsohon alkalin alkalan Najeriya ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa an sanar da rasuwar tsohon alkalin alkalan Najeriya, Mai shari'a Mohammed Uwais.

Mai shari'a Mohammed Uwais ya shafe shekaru da dama yana aiki a Najeriya har ya zamo alkalin alkalai.

Legit ta wallafa cewa marigayin ya jagoranci kwamitin gyaran zabe da Umaru Musa Yar'adua ya kafa domin kawo gyara a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]

OSZAR »