Bangarori 3 da Yan Adawa da Kungiyoyi ke Ganin Gazawar Gwamnatin Tinubu a Shekaru 2
A cikar shekara biyu da hawansa mulki, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fuskanci suka daga manyan adawa, kungiyoyi masu zaman kansu wasu daga cikin dattawan kasar nan.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – A cikin watan Mayu 2025, Atiku Abubakar da Buba Galadima sun bayyana damuwarsu game da wasu fannoni da suka ce gwamnatin Tinubu ta yi watsi da su.

Asali: Facebook
Baya ga su, wasu kungiyoyi sun caccaki tsari da salon mulkin gwamnatin APC da Bola Tinubu ya shekara biyu yana jagoranta.
Wasu daga cikin fannonin da suke ganin an gaza sosai sun hada da:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
1. An ga gazawar Tinubu a fannin tattalin arziki
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da lalata tattalin arzikin Najeriya.
Yana ganin gwamnati ta gaza kawo cigaba mai ma'ana ta fuskar bunkasa tattalin arziki, duk da ikirarin da take yi na kawo gyara a fannin.
Ya ce:
“Wannan gwamnati na tafiyar da kasa ba tare da tsari ko hangen nesa ba. Hauhawar farashin kaya da faduwar Naira sun wuce kima.”
Ya kara da cewa dukkanin manufofin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ya kare ne a kan talakawa tare da kara jefa su a cikin matsi da rashin tabbas.
Ba Atiku Abubakar ne kawai ke kallon tattalin arziki ya lalace ba, jigo a NNPP, Injiniya Buba Galadima na ganin jama'a sun shiga halin ni 'yasu.
A kalamansa:
'Mu ba mu ga komai ba, mun ga ci baya domin abin da N10 za ta saya ma a da yau N1,000 ma ba za ta iya saya maka ba."
2. Amnesty Int'l, Afenifere sun koka da tsaro
Kungiyar ci gaban Yarbawa ta Afenifere ta caccaki Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bayan ya cika shekaru biyu, musamman a bangaren tsaro, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
A cikin sanarwar da suka mikawa manema labarai, shugaban tsagin Afenifere, Oba Oladipo Olaitan, da sakataren yada labarai na kasa, Justice Faloye, kungiyar ta ce akwai matsala.
Sanarwar ta ce:
"Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin da kin mika ikon kafa ‘yan sanda ga jihohi, duk da matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara."
A bangaren Amnesty Int'l, ta ce mutanen da aka kashe a shekaru biyu na mulkin Tinubu sun haura 10,000.
Shugaban kungiyar reshen Najeriya, Isa Sanusi ya ce:
"Yau shekaru biyu kenan da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki da alkawarin inganta tsaro. Amma maimakon hakan, lamarin ya kara tabarbarewa, domin gwamnati ta kasa kare hakkin 'yan Najeriya.”
3. PDP: "Gwamnatin Tinubu ta karo talauci"
Sahara reporters ta wallafa cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta caccaki salon mulkin Shugaba Bola Tinubu, wanda ta ce ya karo talauci da matsi a tsakanin talakawa.
A sanarwar da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, ya sanya wa hannu, ta zargi gwamnatin APC da kara tsananta halin matsin tattalin arziki da kuma tabarbarewar tsaro a fadin ƙasa ta hanyar “wawurar dukiyar ƙasa.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Jam’iyyarmu na cikin damuwa matuƙa da yanayin bakin ciki da rashin kwanciyar hankali da ya mamaye ƙasa baki ɗaya; yadda rashin tsaro ke ta'azzara har ta kai Najeriya ta koma filin kisar jama'a, inda ‘yan ta’adda da ‘yan fashi ke kashe-kashe ba tare da tsoro ba; da kuma matsanancin halin rayuwa da wahalhalun da mutane ke ciki, sakamakon yadda gwamnatin APC ke tafiyar da kuɗin ƙasa cikin rashin tausayi.”:
Jam'iyyar ta shawarci gwamnatin da ta yi amfani da sauran shekaru biyu da suka rage a wa'adinta wajen samawa yan Najeriya rangwamen halin da suke ciki.
Abin da ta mai sharhi ke cewa kan Tinubu
Wani mai bibiyar al'amuran yau da kullum a Kano, Salihu Yusuf Yakasai ya ce abin da Afenifere ta fada a kan mulkin Tinubu yana kan hanya

Asali: Facebook
Ya ce a siyasar kasar nan, ba sabon abu ba ne don kungiyar Afenifere ta caccaki gwamnatin Tinubu, ganin cewa babu karya a cikin abubuwan da ta koka a kansu.
Ya ce:
"Kowa a kasar nan ya san ana shan wahala, amma abin da zai dauki hankali shi ne yadda Afenifere ta caccaki shugaban kasa da ya fito daga yankinta"
Salihu Yusuf Yakasai ya kara da cewa kila wahalar da ta yi katutu na daga cikin abin da yasa yan adawa suka cure wuri guda domin kalubalantar gwamnatin tun yanzu.
Tinubu: Atiku ya yi magana kan zaben 2027
A baya kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce zaben 2027 zai zama tamkar kuri’ar raba gardama da za ta tantance yadda Bola Tinubu ya yi mulki.
Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da jam’iyyar APC ta zarge shi da kokarin farfado da adawa don cimma manufar kashin kansa, ba kishin talakawa ba.
A martaninsa, Atiku ya ce yanzu haka Najeriya ta zama matattarar talauci da fatara da rashin bunkasar tattalin arziki, saboda haka yan Najeriya za su yi alkalanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng