Sarki Sanusi Ii Ya Yi Tattaki da Ƙafa na Sama da Kilomita 1 Ranar Sallah a Kano, An Ji Dalili

Sarki Sanusi Ii Ya Yi Tattaki da Ƙafa na Sama da Kilomita 1 Ranar Sallah a Kano, An Ji Dalili

  • Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya tattaki daga fada zuwa filin idi na Ƙofar Mata domin limancin babbar sallah
  • An ruwaito cewa Sanusi II ya yi tafiyar sama da kilomita ɗaya a ƙafa ne saboda dalilai na tsaro a ranar Sallah
  • Basaraken ya fuskanci matsala a ƙaramar sallah lokacin da ya hau doki zuwa masallacin idi, lamarin da ya zama ajalin mutum ɗaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Sarki na 16 na Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, a ranar Juma’a, 6 ga watan Yuni, ya yi limancin sallar idi a filin idi na Kofar Mata.

Rahotanni sun bayyana cewa Sanusi II ya taka da ƙafarsa, tun daga fadar Kofar Kudu zuwa filin idi na Ƙofar Mata, inda ya jagoranci sallah raka'a biyu ta Eid-el-Kabir.

Sarki Sanusi II ya yi tattaki.
Muhammadu Sanusi II ya yi tafiyar ƙasa ta sama da kilomita 1 daga fadarsa zuwa filin Ƙofar Mata Hoto: @Masarautarkano
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Sarki Sanusi II ya yi tafiya mai tsawon sama da kilomita ɗaya daga fadarsa zuwa filin idi a ranar Babbar Sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sanusi II ya yi tattaki zuwa filin idi a Kano

Basaraken ya gujewa hawa doki kamar yadda aka saba a al’ada, yana mai nuna tawali’u da kuma la’akari da barazanar tsaro.

Idan zaku iya tunawa a lokacin sallar Eid-el-Fitr da ta gabata watau ƙaramar sallah, Sanusi ya hau doki, wanda hakan ya jawo aka farmaki ayarinsa, yayin dawowa daga filin idi.

Wannan al'amari dai ya yi sanadin mutuwar mutum guda, hakan ya sa rundunar ƴan sandan Kano ta sha alwashin gudanar da bincike.

Dalilin da ya hana Sanusi II hawa doki

Haka kuma, hukumomin tsaro a Kano sun ci gaba da jaddada dokar haramta duk wani nau'in hawan doki ko hawan sallah a lokacin Sallah, bisa dalilai na tsaro.

A cikin hudubar da ya yi bayan sallar, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’ummar Kano da su kara ba jami’an tsaro haɗin kai wajen yaki da matsalolin tsaro.

Basaraken ya buƙaci mutanen Kano su ba da haɗin kai don kawo ƙarshen tashe-tashen hankula daga kungiyoyin ‘yan daba, musamman a cikin matasa.

Sarki Sanusi ya yi limancin sallar idi.
Muhammadu Sanusi ya ja hankalin jama'a kan muhimmancin ba jami'an tsaro haɗin kai Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Manyan jami'an gwamnatin Kano sun halarta

Sallar ta samu halartar manyan jami'an gwamnatin Kano ciki har da Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo

Sauran waɗanda aka gani a filin idin sune Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Umar Faruq, mambobin majalisar zartarwa ta jihar, hakimai da sarakuna, da kuma dubban al’ummar musulmi.

A yayin dawowarsa daga filin Idi, Sarki Sanusi ya koma a cikin mota, yayin da tarin mabiya suka rufa masa baya a ƙafa zuwa fadarsa, kamar yadda Punch ta rahoto.

Wani ɗan Kwankwasiyya da ya yi idi a Kofar Mata ya shaida wa Legit Hausa cewa mai martaba mutum ne mai son zaman lafiya.

Malam Sani Abdullahi ya ce ba su ji daɗin hana hawan sallah da aka yi ba domin al'ada ce da ta jima kuma tana ɗaya daga cikin shagulgulan da mutane ke yi ɗa sallah.

"Kowa ya san Sarki ba mai son tashin hankali ba ne, wannan abun kaɗai ya kamata gwamnatin tarayya ta gane idan ma akwai barazanar tsaro ba shi ne ke haddasa ta ba.
"Ba mu jin daɗin hana ahawan sallah, al'ada ce da nuke alfahari da ita ba a Kano kaɗai ba, a Arewa baki ɗaya," in ji shi.

Muhammadu Sanusi II ya janye hawan sallah

A wani rahoton, kun ji cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya soke hawan Sallah da ya fara shirin yi a jihar.

Da yake jawabi a fadarsa da ke ƙofar Kudu ranar jajibirin sallah, Muhammadu Sanusi ya ce ya soke hawan sallah ne domin guje wa tayar da zaune tsaye.

Basaraken ya ɗauki wannan matakin ne bayan rundunar ƴan sanda ta sake jaddada cewa dokar da ta ƙaƙaba ta haramta hawan sallah tana nan daram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »