Abdusamad BUA Ya Faɗi Cigaban da Suka Samu bayan Hawan Tinubu Karagar Mulki

Abdusamad BUA Ya Faɗi Cigaban da Suka Samu bayan Hawan Tinubu Karagar Mulki

  • Shugaban kamfanin BUA a Najeriya, Abdul Samad Rabiu, ya yi magana kan salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Rabi'u ya yaba da shugabancin Tinubu, yana cewa mulkinsa ya kawo ci gaba sosai da sauyi cikin sauri a kasar da ke shan fama da komadar tattalin arziki
  • BUA ya fadi hakan ne a lokacin kaddamar da hanyar tashar jiragen ruwa ta Lekki, inda ya yaba ayyukan tituna daga Lagos zuwa Calabar da Sokoto zuwa Badagry

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya sake yin magana kan salon shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

BUA ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu, yana cewa gwamnatinsa ta kawo ci gaba cikin sauri a Najeriya.

BUA ya yabawa mulkin Tinubu
Abdul Samad BUA ya yabi ayyukan ci gaba na Tinubu. Hoto: @BUAGroup.
Asali: Twitter

Rabi'u ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da hanyar tashar jiragen ruwa ta Lekki, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Yadda BUA ke yabawa salon mulkin Tinubu

Hamshakin dan kasuwar ya sha yabon Bola Tinubu kan tsare-tsaren tattalin arziki da ya dauka a Najeriya bayan hawansa mulkin kasar.

BUA ya ce matakan da Bola Tinubu ke ɗauka sun zama dole ta yadda babu wata hanyar kauce musu idan har ana son gyara komadar tattalin arziki.

Musamman ya yabawa shugaban kan cire tallafin man fetur da daidaito a farashin Naira inda ya ce ba kowa zai iya daukar irin matakan ba saboda yanayin kasar.

Yan Najeriya na cikin wani halin kunci

Kalaman attajirin na zuwa ne a daidai lokacin da su kuma yan kasa ke kokawa kan halin kunci da suka tsinci kansu a ciki na matsin tattalin arziki.

Mafi yawan yan kasar sun sha nuna damuwa kan mulkin Tinubu duba da matsin tattalin arziki wanda kullum ke kara farashin kayayyakin masarufi a kasar.

Ana cikin matsin tattalin arziki kuma sai rashin tsaro ya kara ƙamari wanda ya kuma rikita yan kasar musamman daga yankin Arewacin Najeriya.

BUA ya kwarara yabo ga Tinubu
Abdul Samad BUA ya yabawa ayyukan alherin Bola Tinubu. Hoto: BUA Group.
Asali: UGC

BUA ya fadi ci gaban da aka samu a kasa

Fitaccen dan kasuwar ta fadi alherin Tinubu ne yayin kaddamar da aikin 'Deep Seaport' da shugaban ya jagoranta a Lagos ranar Alhamis 5 ga watan Yunin shekarar 2025 da muke ciki.

A cewar Abdul Samad Rabiu, hanyar gabar tekun Lagos-Calabar, titin Sokoto-Badagry da sauran manyan ayyuka da Shugaban kasa ya faro sun nuna kishinsa na ci gaba.

Ya ce:

“Jagorancinka ya kawo ci gaba na gaske kuma cikin gaggawa, hanyar Lagos-Calabar na tafiya, aikin Sokoto-Badagry yana samun ci gaba.
“Mai girma Shugaba, wannan ci gaban ya yiwu ne saboda kishinka ga sababbin tsare-tsare da dorewar shugabanci."

Farashin shinkafa: BUA ya gana da Tinubu

A baya, mun ba ku labarin cewa kamfanonin BUA da Dangote sun amince da daidaita farashin siminti ga dukkan ‘yan kwangila da ke aiki ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce wannan matakin yana daga cikin gudunmawar da suke bayarwa wajen tallafawa kokarin farfado da tattali.

Abdul Samad Rabiu ya bayyana cewa farashin kayan abinci ya ragu sosai idan aka kwatanta da bara, sakamakon shigo da kayayyaki daga ketare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a [email protected].

OSZAR »