Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin Mayakan ISWAP, an Tura Miyagu zuwa Barzahu

Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin Mayakan ISWAP, an Tura Miyagu zuwa Barzahu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun nuna bajinta yayin da suka daƙile wani harin da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai a jihar Borno
  • Sojojin sun fatattaki ƴan ta'addan ne bayan sun yi yunƙurin kutsawa cikin sansanin ƴan gudun hijira da ke Mallam Fatori
  • Bayan an kwashi dogon lokaci ana musayar wuta, sojojin sun hallaka wasu daga cikin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun daƙile wani mummunan harin mayaƙan ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun daƙile harin ne wanda mayaƙan ISWAP suka kai a sansanin ƴan gudun hijira da ke Mallam Fatori, jihar Borno.

Sojoji sun dakile harin ISWAP a Borno
Dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Sojoji sun gwabza da mayaƙan ƙungiyar ISWAP

Majiyoyin sun bayyana cewa harin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, lokacin da fiye da mayakan ISWAP 150 suka kai farmaki daga yankin Kaniram zuwa wurin da sojoji ke tsarewa.

Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan sun iso a ƙafa, suna harba bindigogi masu nakiyoyi, tare da amfani da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai zuwa inda sojojin suke.

Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa ta hanyar amfani da ƙananan bama-bamai da tankuna, inda suka kai farmaki a inda mayakan ke ƙoƙarin kutsa kai, musamman daga gefen yamma.

Dakarun sojoji sun daƙile harin ISWAP

A cewar majiyoyi, bayan musayar wuta mai zafi da ta ɗauki kusan awa huɗu, mayakan sun samu nasarar kutsa wani yanki na katangar sansanin ƴan gudun hijirar.

Sai dai sojoji ba su ɓata lokaci ba wajen sake tashi tsaye da kuma tinkarar mayakan da ƙarfin wuta fiye da na su, wanda hakan ya tilasta su ja da baya cikin ruɗani.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa an daƙile harin cikin nasara kuma sojoji sun dawo da zaman lafiya a sansanin.

Sojoji sun dakile harin 'yan ISWAP a Borno
Dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An ƙwato tarin makamai a hannun ƴan ta'adda

A halin yanzu, an tabbatar da kashe mayakan ISWAP guda 12, yayin da aka kmƙwato bindigogi AK-47 guda bakwai, manyan bindigogin GPMG guda uku, da rokokin RPG guda biyu, tare da wasu abubuwan fashewa daga hannun maharan.

Majiyoyin sun ƙara da cewa, ko da yake ana cikin hali na fargaba a yankin, an sanya dukkan sojoji cikin shirin ko-ta-kwana don hana wani sabon hari.

Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram

A wani labarin kuma., kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani babban kwamandan ƙungiyar ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Sojojin sun hallaka kwamandan ne bayan sun kai wani farmaki a maɓiyar ƴan ta'addan da ke ƙaramar hukumar Kukawa.

Hakazalika, jami'an tsaron sun hallaka wasu da yawa daga cikin mayaƙansa tare da ƙwato makamai masu tarin yawa a yayin arangamar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »