Kano: Duk da Janye Hawa, Fadar Aminu Ado ta Fitar da Jadawalin Shagalin Sallah
- Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero zai jagoranci Sallar Idi da karɓar gaisuwar Sallah na tsawon kwanaki
- Wannan na kunshe a cikin wani jadawali da aka fitar bayan Aminu Ado Bayero ya goyi bayan haramta hawan Sallah
- A cikin kwanaki hudu da za a shafe kwanaki biyar ana gudanarwa, babu inda aka nuna Basaraken zai yi hawa ko zai bar fadarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Fadar Nasarawa a jihar Kano ta fitar da cikakken jadawalin bukukuwa da tarukan da za su gudana a lokacin Babbar Sallah ta shekarar 2025.
Wannan na zuwa ne bayan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana janye duk wani hawan Sallah, tare da goyon bayan haramta hawa da 'yan sanda suka yi.

Asali: Facebook
A wani jadawali da wani Ali Fagge ya wallafa a shafinsa na X, fadar Nasarawa za ta gudanar da bukukuwan daga ranar Alhamis, 5 ga Yuni zuwa Litinin, 9 ga Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sarki Aminu Ado zai yi bikin Sallah
A cikin jadawalin da Legit Hausa ta gani, an shirya muhimman ayyuka da suka hada da fitowar Sarki, gudanar da sallar idi, da kuma karbar gaisuwar manyan baki daga cikin gida da wajen Kano.
Jadawalin ya nuna cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, shi ne zai jagoranci mafi yawan tarukan.
Jadawalin ya nuna cewa za a shafe kwanaki ana shagalin Sallah babba, yayin da Sarki Aminu Ado Bayero zai karbi gaisuwa daga fadawa da sauran talakawansa.
Jadawalin ya kunshi:
1. Alhamis, 5 ga Yuni 2025 - Ranar Arfa
10.00 n.s – Shigowar Hakimai don gaisuwa da karɓar umarni
10.30 n.s– Fitowar Mai Martaba Sarki
9:00pm – Zaman gaisuwa/fadancin dare
2. Juma’a, 6 ga Yuni 2025 - Ranar Sallah
7:.50 n.s– Fitowar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zuwa masallaci
8.00 n.s – Fara Sallar Idi
8.30 n.s Idar da Salla da Huduba
8.45 n.s – Komawar Sarki cikin fada
9.45 n.s – Gaisuwar manyan baki da jawabai daga Majalisar Sarki
4.25 n.y– Isowar Hakimai don gaisuwar sallah
4.45 n.y – Fitowar Sarki domin karɓar gaisuwar Hakimai
5.45 n.y – Komawar Sarki cikin gida

Asali: Facebook
3. Asabar, 7 ga Yuni 2025
10.30 n.s – Isowar Hakimai daga Nasarawa don barka da sallah
11. 00 n.s – Fitowar Sarki don karɓar gaisuwar baki daga Nasarawa
12.00 n.r – Komawar Sarki cikin fada
4.00 n.y – Wasan al’adun gargajiya
4. Lahadi, 8 ga Yuni 2025
10.00 n.s – Waka daga bakin mawaka da marubuta
4.00 n.y – Halartar Mandiri da sauran shirin nishadi
5. Litinin, 9 ga Yuni 2025
10.00 n.s– Sallamar hakimai
4.00 n.s– Alan waka
Sarki Aminu ya dakatar da hawan Sallah
A wani labarin, mun wallafa cewa Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya fitar da sanarwa kan shirye-shiryen hawan babbar Sallah da za a yi a ranar Juma'a.
Sanarwar ta bukaci dukkannin hakiman masarautar su hallara da dawakansu a cikin birnin Kano ranar Laraba, 4 ga Yuni, domin shirin hawan Sallah a ranar 6 ga watan Yuni.
Sanarwar da Damakwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya fitar, ta bayyana cewa za a gudanar da taro a fadar Sarki ranar Alhamis, 5 ga Yuni, domin karɓar umarni na gaba.
Asali: Legit.ng