Tawagar Gwamnatin Tinubu Ta Ziyarci Kano bayan Mutuwar Ƴan Wasa 22
- Shugaba Bola Tinubu ya waiwayi waɗanda suka tsira daga haɗarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan wasan Kano 22
- Gwamnatin tarayya ta ce tana ƙoƙarin samar da tsarin tallafi mai dorewa ga iyalan mamatan da waɗanda suka jikkata
- Shugaban hukumar wasanni ta kasa, Shehu Dikko ya fadi haka bayan ya kai ziyara Kano tare da isar da ta’aziyyar Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sha alwashin tallafa wa waɗanda suka tsira daga haɗarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar ’yan wasa da jami’an Kano guda 22.
'Yan wasan da suka mutu a haɗarin motar sun gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta komawa gida bayan halartar gasar wasannin kasa da aka kammala a Abeokuta, jihar Ogun.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar wasanni ta kasa, Shehu Dikko, ne ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaban kasa yayin wata ziyara da ya kai Kano da yammacin ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Gwamnati za ta tallafawa iyalan 'yan wasan Kano
Voice of Nigeria ta ruwaito cewa Shehu Dikko ya ce gwamnatin tarayya na kokarin samar da tsarin tallafawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
A cewar Dikko:
“A madadin gwamnatin tarayya, hukumar wasanni ta kasa, ta miƙa tayin aiki tare da gwamnatin jiha domin gina ingantaccen tsarin tallafi ga iyalan mamatan da kuma tabbatar da lafiyar waɗanda suka tsira daga haɗarin.”
“Wannan wani lokaci ne mai matuƙar baƙin ciki a tarihin wasanninmu. Muna so gwamnatin jihar da iyalan su san cewa muna taya su jimami, kuma za mu yi duk abin da ya kamata."
Gwamnati ta yi jimamin rasuwar 'yan wasan Kano
Dikko, wanda ya dawo daga birnin Landan inda ya halarci wasan ƙarshe na kofin Unity da wasu taruka kan ci gaban wasanni, ya wuce kai tsaye Kano daga filin jirgi bayan isowarsa Najeriya. Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsallam Gwarzo ne ya tarbe shi, kasancewar Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na Saudiyya domin aikin hajji.

Asali: Facebook
Wasu manyan jami’an gwamnati, daga ciki har da Sakataren gwamnatin jiha Umar Farouk Ibrahim, kwamishinoni da shugabannin hukumar wasanni ta Kano, duk sun halarci ganawar.
Shugaban ya kai ziyara gidajen wasu daga cikin iyalan mamatan a cikin birnin Kano daaga bisani ya wuce asibitin Murtala Muhammad inda ake kula da wasu da suka jikkata a haɗarin.
Barau ya yi ta'aziyyar 'yan wasan Kano
A baya, kun ji cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya kai ziyara ta'aziyya ga iyalan 'yan wasa 22 da suka rasu a hadarin mota da ya faru ranar Asabar.
Mutanen da suka rasa 'yan uwansu sun tarbe Sanata Barau a masallacin Juma’a na Gwagwarwa, a karamar hukumar Nasarawa, jihar Kano domin karbar gaisuwa.
Sanata Barau ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi da ya girgiza Najeriya, tare da addu'ar Allah ya gafarta masu, daga baya, ya mika tallafi ga iyalan mamatan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng