Kashim Shettima Ya Dura Mokwa bayan Mutuwar Mutane 200, Ya Miƙa Saƙon Tinubu

Kashim Shettima Ya Dura Mokwa bayan Mutuwar Mutane 200, Ya Miƙa Saƙon Tinubu

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kai ziyara garin Mokwa a jihar Neja domin jajen ambaliyar da ta faru a makon jiya
  • Sanata Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin fitar da Naira biliyan 2 domin gyara gidajen da ruwa ya lalata a Mokwa
  • Gwamnatin Neja ta tabbatar da cewa zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane sama da 200 kuma ana ci gaba da laluben mamata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin fitar da Naira biliyan biyu (₦2bn) nan take domin sake gina gidajen da ambaliya ta rushe a garin Mokwa, jihar Neja.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara garin domin ta'aziyya da jajen ambaliyar da ta afku a makon jiya.

Shettima ya je jaje garin Mokwa a jihar Niger.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim.Shettima ya isa garin Mokwa Hoto: @voiceofnigeria
Asali: Twitter

Sanata Kashim Shettima ya ce bayan waɗannan kudi, Shugaba Tinubu ya kuma amince a fitar da tirela 20 na shinkafa domin rabawa waɗanda ibtila'in ya shafa, in ji Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Shettima ya isar da saƙon Tinubu a Mokwa

Mataimakin shugaban kasar ya tabbatarwa al'ummar garin Mokwa cewa zuciyar Tinubu na tare da su kuma gwamnatin tarayya za ta magance duka matsalolin da suka addabe su.

Har ila yau, Shettima ya ce mai girma shugaban ƙasa ya ba da umarnin gyara gadojin da ambaliyar da lalata cikin gaggawa don mutane su ci gaba da harkokinsu.

Haka zalika, ya ce an umurci a gyara dukkan bututun ruwa da suka lalace a garin Mokwa domin hana sake aukuwar irin wannan bala’in nan gaba.

Mutane sama da 200 sun mutu a garin Mokwa

Sama da mutane 200 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon ambaliyar ruwa da ta ɓarke a garin Mokwa bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a daren Laraba, 28 ga watan Mayu.

Kwamishinan Harkokin Jin Kai na Jihar Neja, Ahmad Suleiman, ya ce zuwa yanzu, sama da gawarwaki 200 aka riga aka gano, wasu da dama sun ɓata.

Ya ce:

“Muna da fiye da gawa 200 da aka gano, amma har yanzu muna ci gaba da neman wasu. Babu wanda zai iya bayyana adadin mutanen da suka mutu a yanzu, domin har yanzu ana ƙara ciro gawarwaki.”
Kashim Shettima ya isar da sakon Tinubu.
Kashim.Shettima ya ce gwamnatin Tinubu zs ta gyara gadoji da gidajen da ambaliya ta shafa a Mokwa Hoto: @Voiceofnigeria
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar ta ce ta fara raba kayan agaji ga wadanda suka rasa matsuguni, waɗanda tuni aka samar masu wurun zama a sansanonin wucin-gadi domin samun kulawa.

A ziyarar da ya kai Mokwa yau Laraba, 4 ga watan Yuni, Kashim Shettima ya tabbatar wa mutanen da ambaliya ta shafa cewa gwamnatin Tinubu na tare da su.

Gwamna Bago ya hana hawan Sallah

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bago ya ba da umarnin taƙaita shagulgulan babbar sallah domin jimamin mummunar ambaliyar da ta afku a garin Mokwa.

Muhammed Bago ya buƙaci duka masarautun jihar Neja su soke duk wani hawam sallah da shagulgulan da suka saba shiryawa saboda haƙin da ake ciki.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, shi ne wanda ya isar da umarnin Gwamna Bago a wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »