EFCC: Ƴan Ƙasar Waje Sun ga Takansu a Najeriya, Kotu Ta Ɗaure Su bayan Kama Su da Laifi

EFCC: Ƴan Ƙasar Waje Sun ga Takansu a Najeriya, Kotu Ta Ɗaure Su bayan Kama Su da Laifi

  • Kotu ta kama wasu ƴan kasar Philippines takwas da hannu dumu-dumu a aikata lafin zamba da ta'addanci ta yanar gizo
  • Hukumar EFCC ce ta gurfanar da waɗanda ake zargin bayan sun shiga hannu a samamen da jami'ai suka kai a jihar Legas
  • Kotun ta ɗaure kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara a gidan yari na tsawon shekara ɗaya ko zaɓin tara na Naira miliyan 1

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a jihar Lagos, ta yanke hukuncin daure wasu mutum takwas 'yan kasar Philippines, kowane shekara daya a gidan gyaran hali.

Kotun ta ɗaure ƴan kasar wajen ne bisa kama su da laifin zamba ta yanar gizo da ta'addancin intanet a Najeriya.

Hukumar EFCC ta yi nasara kan wasu ƴan kasar waje su takwas.
Kotu ta ɗaure ƴan ƙasar waje bisa laifin ta'addancin Intanet a Najeriya Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa watau EFCC ta tabbatar da yanke wa mutanen hukunci a shafinta na X, ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Jerin ƴan kasar wajen da kotu ta hukunta

Mai shari’a Alexander Owoeye ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan da wadanda ake zargin suka amsa laifuffukansu a gaban kotu.

Sunayen wadanda kotun ta yanke wa hukunci sun haɗa da:

1. Beverlyn Casino

2. Mae Eribal

3. Mary Grace Dela Cruz

4. Jamal Polea

5. Tricia Castro

6. Rai Camara

7. Cherry De Leon

8. Danica Jarapan

Wane laifi kotu ta kama mutanen da aikatawa?

Tun farko, hukumar EFCC wacce ta gurfanar da su, ta bayyana cewa ta gano wadanda ake tuhuma na amfani da saƙonni da takardun bogi wajen yaudarar jama'a.

EFCC ta ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake kara, Ms Beverlyn Casino, da laifin shiga cikin tsarin kwamfuta da gangan da nufin lalata tsaron tattalin arziki da zamantakewar Najeriya.

"Wannan ya saba da tanadin sashe na 18 na Dokar Laifukan Intanet ta 2015 da sashe na 2(3)(d) na dokar hana ta’addanci ta 2022," in ji EFCC.

Bayan sun amsa laifukan da ake tuhumarsu, babbar kotun ta ɗaure kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake kara tsawon shekara ɗaya a gidan yari ko a biya tarar Naira miliyan 1.

Hukumar EFCC ta samu nasara a kotun tarayya.
Kotu ta umarci a maida mutanen kasarsu bayan sun gama zaman gidan yari Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Kotun ta umarci a tasa ƙeyarsu zuwa Philippines

Kotu ta umarci shugaban hukumar shige da fice (NIS) da ya kora su zuwa ƙasar su ta Philippines cikin kwana bakwai bayan kammala zaman gidan yari.

Dukkan na’urorin zamani da aka kwace daga hannunsu, kotu ta umarci a mika su ga Gwamnatin Tarayya.

Waɗannan mutum takwas na cikin mutane 792 da dakarun EFCC suka cafke a wani babban samame da suka kai ranar 10 ga Disamba, 2024, a jihar Legas.

Kotu ta ɗaure ɗan damfara na tsawon shekara 63

A wani rahoton, kun ji cewa wata babbar kotu a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta yanke wa wani matashi, Olaniyan Gbenga Amos hukuncin daurin shekaru 63.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Amos ne a gaban kotun da ke Ibadan bisa tuhume-tuhume 30 da suka shafi zamba cikin aminci.

Sai dai kotun ta gamsu ya aikata laifuffuka tara daga cikin waɗanda ake tuhumarsa a kai, sannan ta umarce shi da ya biya diyyar kudin da ya karɓa daga hannun wadanda ya damfara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: [email protected] 07032379262

OSZAR »