DSS da Sojoji Sun Tarfa Yaran 'Dan Ta'adda, Sun Aika Mayakan Dogo Gide 45 Barzahu
- Jami’an tsaro sun kai farmakin bazata a garin Kuchi, dake jihar Neja inda suka hallaka akalla 'yan bindiga 45 da ke karkashin Dogo Gide
- Wata majiyar tsaro ta ce DSS ta gano shirin da Dogo Gide da mabiyansa suka kulla na kai hari, har da gayyato abokansu don kashe bayin Allah
- An gayyato 'yan ta’adda daga jihohin Zamfara da Kaduna, amma jami’an tsaro sun yi musu kwanton-bauna, suka kashe da dama daga cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Hukumar Tsaro ta DSS da sojojin Najeriya sun kashe akalla 'yan bindiga 45 a wani samame da suka kai a kusa da garin Kuchi, karamar hukumar Munya da ke jihar Neja.
An gudanar da wannan aiki ne cikin sirri, kuma hakan na nuna karin nasara a jerin hare-haren da ake kaiwa kan 'yan bindiga a jihar Neja, musamman mabiyan Dogo Gide.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa DSS ta bi sawun 'yan bindigar, hakan ya sa suka hana kai hari a wasu kauyuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
An gano cewa jagoran 'yan bindigar, Dogo Gide, tare da mabiyansa, sun shirya kai hari kan al’ummomi daban-daban.
An kashe yaran kasurgumin ɗan ta’adda
The Nation ta ruwaito wata majiya ta tsaro ta ce binciken sirri da aka gudanar da sababbin dabaru ya gano cewa an gayyato wasu miyagun 'yan ta’adda zuwa jihar Neja domin kai hari.
An gayyato su ne daga dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, da kuma wasu sassa na jihar Kaduna, domin su kai hari a kauyukan da ke yankin Kuchi kamar yadda Dogo Gide ya umarta.

Asali: Facebook
Babbar majiyar ta ce:
“A safiyar Litinin, 2 ga Yuni 2025, wasu 'yan bindiga daga jihohin Kaduna da Zamfara, kimanin 100, dauke da manyan makamai, sun nufi garin Kuchi a karamar hukumar Munya domin kan al’umma.”
DSS da sojoji sun fatattaki 'yan ta’adda
Rahoton ya cigaba da cewa jami’an tsaron Najeriya sun kai farmaki cikin gaggawa, suka yi wa 'yan ta’addan kwanton-bauna. Majiyar tsaron ta ce:
“Amma jami’an tsaro sun kai masu harin bazata, inda suka tare su a wajen garin Kuchi kafin su fara kai hari.
“Jami’an sun fafata da 'yan bindiga, suka kashe da dama daga cikinsu, sannan da dama suka jikkata. Haka kuma an kwato babura da makamai masu yawa daga hannunsu.”
“Amma jami'an DSS guda biyar sun jikkata sosai, kuma a halin yanzu suna asibiti ana kula da su.”
An zargi mutum 2 da assasa ta'addanci
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya zargi tsofaffin gwamnoni biyun da assasa matsalar yan bindiga da yunwa a yankinsu
Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi na Ribas dake sukar Bola Tinubu a yanzu ba su yiwa jama'arsu komai ba a zamaninsu.
A cewar Shehu Sani, waɗannan shugabanni biyu ba su da hurumin sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ganin cewa a sun gaza magance matsalolin a gwamnatocinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng