'Tun a Tafiya Motarmu ke Samun Matsala,' Yar Wasar Kano Ta Fadi 'Dalilin' Hadarinsu
- Dorathy Okwuzuluike, daya daga cikin wadanda suka tsira a hatsarin mota da ta aukawa yan wasan Kano daga Ogun ta fara iya magana
- Ta bayyana cewa a lokacin da mummunan al'amarin ya faru, kujerarta kawai ta iya rikewa kafin daga baya ta farka a asibiti
- Kan abin da ya haddasa hatsarin, ta tabbatar da cewa dama motar tana yawan samun matsala tun a tafiya, haka ma a dawowarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Daya daga cikin wadanda suka tsira daga mummunan hatsarin da ya kashe mutane 22 daga cikin ‘yan wasa da jami’an Kano, Dorathy Okwuzuluike, ta magantu.
Ta bayyana cewa tana zargin hatsarin ya faru ne sakamakon matsalar birkin motar da suke ciki ana tsaka da tafiya.

Asali: Twitter
BBC ta ruwaito cewa hukumar kiyaye hadurra ta Kkasa (FRSC), ta ce hatsarin faru ne da 12:30 na rana a ranar Asabar, a kusa da Gadar Yankifi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Tawagar na kan hanyarta ta dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka gudanar a Abeokuta, kuma mutun 22 ne suka riga mu gidan gaskiya.
Kano: An fara binciken dalilin hatsarin yan wasa
Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar Litinin, FRSC ta ce za ta kaddamar da bincike domin gano musabbabin hadarin.
Amma daya daga cikin wadanda suka tsira, Dorathy, ta bayyana cewa tana zargin matsalar burki ce ta haddasa lamarin.

Asali: Facebook
Da take bayani, Dorathy ta ce:
“Na yi zaton birkin motar ne ya ki aiki ko wani abu makamancin haka. Abin da kawai na iya yi shi ne rike kujera sosai. Wannan ne karshen abin da na tuna. Na farka ne kawai a asibiti.”
“Mun kwashe kwana biyu a hanya a lokacin tafiya, haka ma a lokacin dawowa. Motar tana yawan samun matsala, sai a gyara.”
Hukumar wasannin jihar Kano ta magantu
Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Fagge, ya bayyana cewa har yanzu ba wanda ya gano hakikanin dalilin hatsarin.
A cewarsa:
“Motar tana dauke da mutane 31 kuma wadanda suka tsira suna kujerun baya guda biyu. Daga sauran kujerun zuwa wajen direba, babu wanda ya tsira. Babu wanda zai iya cewa ga yadda abin ya faru. Mu dai mun dauka cewa kaddara ce.”
Sun yi addu'ar Allah Ya jian wadanda suka koma ga Mahaliccinsu a wannan hatsari wanda ya tayar da hankulan jama'a.
NNPP ta fadi dalilin hatsarin 'yan wasan Kano
A baya, kun samu labarin cewa jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa rashin ingantattun hanyoyi ne ya haddasa mummunan hatsarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan wasa 22 daga jihar Kano.
Hatsarin ya faru ne yayin da tawagar 'yan wasan ke dawowa daga gasar wasanni da aka gudanar a jihar Ogun, inda motarsu ta fadi daga gadar Dakatsalle a karamar hukumar Kura.
A wata sanarwa da ya fitar, jigo a jam'iyyar NNPP daga Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya bayyana hatsarin a matsayin abin tausayi, tare da mika ta'aziyyarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng