Bayan Kalaman Wike, Gwamna Fubara Ya Sanya Labule da Shugaba Tinubu

Bayan Kalaman Wike, Gwamna Fubara Ya Sanya Labule da Shugaba Tinubu

  • Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya wanke ƙafa ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamna Simi Fubara ya ziyarci Shugaba Tinubu ne a gidansa da ke jihar Legas a ranar Talata, 3 ga watan Yunin 2025
  • Ziyarar dakataccen gwamnan na zuwa ne a yayin da ake ƙoƙarin sasanta shi da Nyesom Wike kan rikicin siyasar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Gwamna Siminalayi Fubara ya gana da Shugaba Bola Tinubu ne a gidansa da ke Legas, a ranar Talata, 3 ga watan Yunin 2025.

Siminalayi Fubara, Bola Tinubu
Gwamna Fubara ya gana da Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya tabbatar da ganawar a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Gwamna Fubara ya gana da Bola Tinubu

Bayo Onanuga ya bayyana cewa dakataccen gwamnan na jihar Rivers, ya sanya labule da Shugaba Tinubu ne a birnin Legas.

“Gwamna Sim Fubara na jihar Rivers, wanda yanzu haka ke kan dakatarwa daga ofis, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a Legas a ranar Talata."

- Bayo Onanuga

Sai dai, babu abin da ya bayyana a fili har zuwa yanzu kan me aka tattauna tsakanin Shugaba Tinubu da Gwamna Fubara.

Ana ƙoƙarin sasanta Wike da Gwamna Fubara

Wannan ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sulhunta gwamnan da tsohon uban gidansa a siyasa, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

A watan Maris, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers tare da dakatar da Gwamna Fubara daga aiki, bayan da ƙoƙarin sasanta rikicin siyasa a jihar ya ci tura.

Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan daga ofis ne na tsawon watanni shida.

Wannan ganawa na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da Gwamna Fubara ya bayyana cewa ya ajiye girman kai da son rai domin dawo da zaman lafiya a jihar Rivers, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Wike, Fubara
Ana kokarin sulhunta Wike da Gwamna Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamna Fubara ya bayyana cewa yana ƙoƙarin yin sulhu da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Dukkaninsu su biyu sune suka jawo rikicin siyasa da ya haifar da dakatar da majalisar zartarwa da ta dokoki a jihar.

“Dole ne mu sauko daga kan dokin girman kai mu rungumi tsarin sasanci. Kuma wannan shi ne abin da muke yi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ci gaban jihar. Ba game da kai bane, muradin jihar ne ya fi komai muhimmanci."

- Gwamna Siminalayi Fubara

Wike ya magantu kan rikici da Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan birnin tarayya, Abuja, ya yi magana kan rikicinsa da Siminalayi Fubara.

Nyesom Wike ya bayyana cewa akwai lokutan da yake zama ya riƙa zibsr da hawaye saboda irin cin amanar da Gwamna Fubara ya yi masa.

Ministan ga bayyana cewa gwamnan ya bayyana cewa Gwamna Fubara ya bari wasu da suke gaba da shi, suna yaƙarsa ta hannunsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta [email protected]

OSZAR »