Ambaliyar Neja: Sanata Ya Kadu da Mutuwar Mutane 200, Ya Raba Tallafin N50m a Mokwa
- Sanata Abubakar Sani Bello ya bada tallafin N50m domin rage radadin ambaliyar da ta hallaka mutane da lalata gidaje a jihar Neja
- Tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin Adamu Usman ta wakilci tsohon gwamnan wajen isar da sakon ta’aziyya da kuma ba da tallafin
- Sarkin Mokwa ya gode matuƙa bisa gudunmawar, yana mai cewa ambaliyar ta zo wa mutane a ba-zata, kuma ta jawo babbar asara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa kuma shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa, Abubakar Sani Bello, ya kadu da ambaliyar garin Mokwa.
Sanata Abubakar Sani Bello ya ba da tallafin Naira miliyan 50 domin rage radadin ambaliyar da ta hallaka mutane sama da 200, da lalata daruruwan gidaje.

Asali: Twitter
Tawagar sanatan Neja ta isa garin Mokwa
Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Muawiyah Yusuf Muye ya wallafa a shafinsa na X cewa wata tawaga ta musamman ce ta wakilci Sanata Bello zuwa miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Mokwa bisa wannan iftila'i, tare da ba da tallafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Muawiyah Yusuf Muye ya sanar da cewa tsohon shugaban majalisar jihar Neja, Rt. Hon. Adamu Usman ne ya jagoranci tawagar.
Sauran jagororin tawagar sun haɗa da tsohon ɗan majalisar tarayya kuma tsohon shugaban ma’aikata na Sanata Bello, Hon. Mikhail Al-Amin Bmitosahi.
Sanarwar ta ce an karɓi baƙuncin wannan tawagar ne a fadar Ndalile na Mokwa, Alhaji Shaba Aliyu, ta hannun mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Mokwa.
Sanata ya ba da tallafin N50m ga Mokwa
Da yake jawabi a madadin sanatan, Adamu Usman ya miƙa saƙon ta’aziyyar Sanata Bello ga mutanen yankin Mokwa, yana mai cewa:
“Sanata Sani Bello ya ce mu zo a madadinsa don miƙa gaisuwar jaje da ta’aziyya ga jama’ar Mokwa. da kuma ba da tallafin Naira miliyan 50.
“Duk da kasancewar yanzu yana cikin aikin Hajji a ƙasar Saudiyya, amma har yanzu yana cikin juyayi da alhini bisa wannan ibtila’i da ya faru.”
Adamu Usman ya ƙara da cewa Sanata Bello ya jadda muhimmancin kai dauki ga wadanda iftila'in ambaliyar ya shafa a Mokwa domin rage masu radadi.
Sanatan ya kuma yi addu’ar samun rahamar Allah ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma samun addu'ar Allah ya maye gurbin dukiyar da aka yi asararta.

Asali: Twitter
Basarake ya yi magana kan ambaliyar Mokwa
Da yake mayar da martani a madadin al’ummar Mokwa, sarkin yankin ya bayyana matuƙar godiya ga Sanata Bello bisa wannan tallafi da ya bayar.
Alhaji Shaba Aliyu ya ce:
“Muna godiya ƙwarai da wannan ziyara da kuma gudunmawar sanatan. Ko da yake lamarin ya zo mana a ba-zata, amma mun karɓi wannan iftila'i a matsayin ƙaddara daga Allah.
“Ba mu taba fuskantar irin wannan ambaliya a tarihin garinmu ba, ba mu da wani babban kogi da za mu ce shi ne ya cika ya batse har ya jawo ambaliyar."
Basaraken ya ce mutane sun tsinci kansu ne kawai a cikin wannan ambaliyar, wacce ta jawo asarar rayuka da lalata muhallin dubunnan mutanen garin.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Jihohi 8 da za a iya samun ambaliya a Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a wasu jihohi a watan Yuni 2025, sakamakon ruwan sama mai yawa a tsakiyar damina.
Jihohin da ambaliya ke da yuwuwar faruwa sun haɗa da Kano, Kaduna, Neja, Nasarawa, Kwara, Sokoto, Filato sai kuma birnin Abuja, inda aka hango ruwan sama mai ƙarfi.
NiMet ta shawarci manoma da su ɗauki matakan kariya, su share magudanan ruwa tare da amfani da sabbin dabarun noma da suka dace da sauyin yanayi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng