An Yi Karar Wike wajen Tinubu kan Zargin Kashe Kudin Gwamnati ba Bisa Tsari ba
- Wani lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam ya roƙi Bola Tinubu da ya dakatar da tattaunawar da Nyesom Wike ke yawan yi a kafafen labarai
- Ya bayyana cewa tattaunawar ba ta da amfani illa ɓarnatar da kuɗin jama’a a lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin tsananin ƙuncin rayuwa
- Lauyan ya ce kuɗin da Ministan ke kashewa a wata-wata na iya taimaka wa ɗaruruwan marasa galihu da ‘yan gudun hijira a faɗin ƙasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wani sanannen lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Ifeanyi Ejiofor, wanda kuma shi ne lauyan ƙungiyar IPOB ya yi tsokaci kan aikin Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Lauyan ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da shahararren shirin tattaunawar watan-wata da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ke gudanarwa.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa Ejiofor ya yi kira ga Bola Tinubu ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Rahotanni sun nuna cewa ya yi magana yana mai cewar shirin ba ya ƙunshe da wani muhimmin abu face ɓarnatar da kuɗin jama’a tare da bai wa Wike damar nuna isa.
Ya ce hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da hauhawar farashi, rashin wadataccen albashi da kuma ƙarin talauci.
A saboda haka ne lauyan ya bayyana shirin a matsayin wani al’amari na nuna rashin damuwa da halin da jama’a ke ciki.
An zargi Wike da kashe makudan kudi
A cewar Ejiofor, yawan kuɗin da ake kashewa wajen shiryawa da watsa tattaunawar Wike a wata-wata zai iya kai ɗaruruwan marasa galihu ga samun mafita a fannoni da dama.
PM News ta wallafa cewa lauyan ya ce:
“Yayin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da talauci, matsanancin tsadar rayuwa da rashin kula da lafiya da ilimi,
"Ana zargin cewa ana kashe daruruwan miliyoyin Naira kowane wata wajen shirya wannan shiri da bai da wani amfani ga jama’a,”
Ya ƙara da cewa:
“Kuɗin da ake kashewa a shirye-shiryen nan na iya gyara makarantu, samar da abinci da asibitoci ga mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira,
"Ko kuma gina matsuguni ga waɗanda ambaliya ta rusa gidajensu a Jihar Neja.”
An bukaci Tinubu ya dakatar da Wike
Lauyan ya bayyana cewa abin da ‘yan Najeriya ke buƙata ba ɗaukaka da watsa shirye-shirye ba ne, sai dai shugabanci na gari, gina tattali da kuma mayar da hankali kan bukatun al’umma.
Ya roƙi Shugaba Tinubu da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin kawo karshen abin da ya kira almubazzaranci.

Asali: Facebook
A cewar lauyan:
“Ya kamata shugaba Tinubu ya dakatar da wannan almubazzarancin da Wike ke yi, a mayar da hankali kan ayyukan ci gaban jama’a."
Musulman Abuja sun yi korafi kan Wike
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Musulman Abuja ta bukaci Nyesom Wike ya dakatar da aikin gyaran ruwan Abuja.
Kungiyar ta ce bai dace a fara aikin da zai jawo katse ruwan sha a daidai lokacin da Musulmai za su yi bikin sallah ba.
Nyesom Wike ya fara aikin gyaran ruwan a sassan Abuja kuma ya bayyana cewa aikin zai dauki tsawon mako biyu ana yinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng