'Yan Bindiga Sun Kai Zafafan Hare Hare a Benue, Sun Kashe Sama da Mutane 40

'Yan Bindiga Sun Kai Zafafan Hare Hare a Benue, Sun Kashe Sama da Mutane 40

  • Aƙalla mutum 43 ne aka kashe a hare-haren Gwer ta Yamma da Apa a jihar Benue, mako guda bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 40
  • Maharan sun kai hari garin Tse Antswam da Edikwu Ankpali, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, suka kashe mutum fiye da 43
  • Mahukunta sun tabbatar da hare-haren, kuma an ce har yanzu ana kan neman wadanda suka bace yayin da 'yan sanda ke yin bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Aƙalla mutum 43 ne aka kashe a sababbin hare-hare da aka kai kan garuruwan ƙananan hukumomin Gwer ta Yamma da Apa da ke jihar Benue.

An kaddamar da mummunan hare-haren ne a yammacin ranar Lahadi, mako guda kacal bayan kashe sama da mutum 40 a Gwer ta Yamma, ciki har da ɗan sanda.

'Yan bindiga sun kai sababbin hare-hare a jihar Benue, an kashe akalla mutane 43
Gwamnan Benue, Hyacinth Iormem Alia, ya gana da shugabannin sojoji kan tsaro a jihar. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

Benue: An kashe mutum 18 a Tse Antswam

Wasu mazauna yankin sun shaida wa jarida Daily Trust a Makurdi cewa maharan sun dura garin Tse Antswam, da ke gefen garin Naka a ta Yamma da misalin ƙarfe 7:00 na yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Rahoton jaridar ya nuna cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da suka shiga garin Tse Antswam, ina suka kashe aƙalla mutum 18.

Wadanda suka tsira daga harin sun ce mazauna kauyen da dama sun tsere zuwa dazuka, wasu kuma sun fada rijiyoyi domin su tsira daga harin.

An kashe fiye da mutum 25 a Edikwu Ankpali

Sarkin gargajiya na yankin, Ter Nagi, Chief Daniel Abomtse, ya tabbatar da yawan waɗanda aka kashe, inda ya bayyana harin a matsayin "salon farmakin ‘yan tawaye".

A cewarsa Abomtse:

“Da safiyar nan mun gano gawarwaki 18. Akwai wadanda suka jikkata, da muke fargabar ba lallai su kai labari ba. Har yanzu ana ci gaba da neman waɗanda suka ɓace.”

Sarkin yankin ya ce sun yi mamakin irin ƙarfin halin 'yan bindigar na kai hari ƙauyen Tse Antswam, kasancewar yana kusa da wani shingen soja da ke kan titin Naka–Makurdi.

A ƙaramar hukumar Apa kuwa, lamarin ma ya kasance mai muni, inda 'yan garin suka bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye Edikwu Ankpali, suka kashe fiye da mutum 25.

'Yan bindiga sun farmaki kananan hukumomin Benue inda suka kashe sama da mutane 40
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Benue a Arewa ta Tsakiyar kasar. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan sanda sun tabbatar da hare-haren Benue

Wani mazaunin yankin mai suna Tony ya shaida wa manema labarai ta waya cewa:

“Mun ƙirga fiye da gawarwaki 25 a Edikwu Ankpali. Ana shirin yin jana'izar wasu daga cikinsu.”

Tsohon jami’in gwamnati, John Ikwulono, ya ƙara da cewa an sake kai hari a Opaha da Asubahin ranar Litinin, amma ba a tabbatar da yawan waɗanda aka kashe ba.

A cewarsa:

“Yanzu haka mutane sun makale a Odugbo. Ba sa iya tserewa daga harin 'yan bindigar. An binne Mutum 11 da aka kashe a Edikwu, amma wawan matattu yana ƙaruwa.”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Benue, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da faruwar hare-haren, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda suka mutu ba.

'Yan bindiga sun budewa sojoji wuta a Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun hallaka mutum huɗu, ciki har da sojoji biyu, a wani hari da suka kai Ijaha Ikobi, jihar Benue.

Rahotanni sun ce sojojin sun fada tarkon 'yan bindigar ne a lokacin da suka isa Ijaha Ikobi domin kai daukin gaggawa, inda maharan suka yi musu kisan gilla.

Shugaban ƙaramar hukumar Apa ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an kwashe gawarwakin sojojin da sauran waɗanda suka mutu daga wurin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

OSZAR »