Gombe: Bayan Kashe Babban 'Dan Sanda a Kano, Yan Kalare Sun Tasamma Hallaka DPO
- Rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ƙungiyar Kalare a Gombe, inda aka kai wa babban dan sanda, CSP Adamu Alhaji-Idi farmaki
- Lamarin ya afku ne ana tsaka da taron sulhu tsakanin kungiyoyin yan daban, sai suka hade kai tare da kai wa DPO hari
- Rundunar ‘yan sanda ta Gombe ta tabbatar da cafke mutane 25 da ake zargi da hannu a harin, kuma ana ci gaba da bincike
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Taron sulhu tsakanin ɓangarori masu adawa a cikin ƙungiyar Kalare da ke Kwadon, ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba a jihar Gombe ya rikide zuwa tashin hankali.
Lamarin ya juye a daidai lokacin da daban jiya kan shugaban sashen ‘yan sanda na Kwadon (DPO), CSP Adamu Alhaji-Idi, kuma suka yi masa jina-jina rai a hannun Allah.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne a lokacin da ake ƙoƙarin sasanta ɓangarorin, sai kawai suka hade kai, suka kuma kai hari a kan DPO.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
An yiwa DPO jina-jina a Gombe
Rahoton ya cigaba da cewa CSP Adamu Alhaji-Idi ya samu munanan raunuka kuma na garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe domin kulawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, inda ya bayyana cewa an kama mutum 25 da ake zargi da hannu a harin.
Ya ce:
“Rundunar ‘yan sanda ta Gombe na Allah wadai da harin da aka kai wa wani babban jami’in ‘yan sanda mai aiki a matsayin DPO kuma muna tabbatar wa jama’a cewa muna ci gaba da bincike domin gurfanar da masu laifi.”
An aika jami'an tsaro zuwa Gombe
DSP Abdullahi ya bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa daga Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da ayyukan tsaro misalin karfe 9:00 na safe, kan batun.
Ya bayyana cewa nan take aka tura tawagar jami’ai daga sashin Operation Hattara ƙarƙashin jagorancin CSP Ali Madaki zuwa wurin.
Ya ce:
“Jami’ai sun kama mutum 25 da dukkanninsu mazauna Kwadon ne. Yanzu haka suna hannun ‘yan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da binciken sirri. Bayan kammala binciken za a gurfanar da su a gaban kotu.”
Ya ƙara da cewa rundunar ba za ta lamunci hare-hare ga jami’an tsaro ba, kuma za ta tabbatar da cewa dokar ta yi aiki a kan duk wanda aka kama da laifi.

Asali: Facebook
DSP Abdullahi ya ce:
“Zamanin kai wa jami’an tsaro hari ba tare da hukunci ba ya ƙare. Rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da ganin an yi adalci da wanzar da zaman lafiya a jihar Gombe,”
Kano: An kama wadanda suka kashe dan sanda
A baya, mun wallafa cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke mutane 41, daga ciki har da wanda ake zargi da hannu a kisan CSP Baba Ali, DPO na Rano.
An kashe CSP Baba Ali yayin da yake bakin aikinsa a yankin Rano, kuma bayan faruwar lamarin, rundunar 'yan sanda ta tura jami'anta na musamman domin gudanar da bincike.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya bayyana cewa rundunar ba za ta yarda da irin wannan ta'asa ba, kuma za ta tabbatar an dauki matakin doka.
Asali: Legit.ng