Sanata Ya Fadi yadda ake Kara Karfin Boko Haram don Dagula Mulkin Tinubu
- Orji Uzor Kalu ya zargi wasu jiga-jigan siyasa da tallafawa Boko Haram don haddasa rashin zaman lafiya a gwamnatin Bola Tinubu
- Sanatan ya ce akwai masu mulki, 'yan kasuwa da manyan ma'aikata da ke amfani da ta’addanci don su samu madafun iko da shugabanci
- Maganar Sanata Kalu ta biyo bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a Borno wanda ya yi sanadin mutuwar fasinjoji tara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Abia kuma Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya zargi wasu masu fada-a-ji a siyasar Najeriya da daukar nauyin Boko Haram.
Ba tare da kawo wasu hujjoji ba, Sanata Kalu ya ce ana daukar nauyin 'yan ta'addan ne don hana gwamnatin Bola Ahmed Tinubu nasara.

Asali: Facebook
Sanata Kalu ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels Television, inda ya bayyana cewa hare-haren kungiyar na da nasaba da siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Zargin ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsanancin rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Gabas.
'Yan siyasa na da hannu a Boko Haram,' Kalu
Sanata Kalu ya bayyana cewa akwai wasu 'yan siyasa da ke amfani da kungiyoyin 'yan ta'adda kamar Boko Haram don rusa gwamnati da hana shugaba Tinubu cimma nasara.
Kalu ya ce:
“Wannan ba wai matsalar tsaro ce kawai ba, matsalar siyasa ce.
"Wasu daga cikin waɗanda ke da karfin fada a ji suna amfani da ta’addanci a matsayin makami na yakar gwamnati, ba wai don samun kudi ba, sai don kwace mulki.”
Ya kara da cewa har yanzu akwai wasu manyan jami’an gwamnati da ke taimaka wa masu tada kayar baya don cika burinsu na samun mulki ta kowace hanya.
'Rashin tsaro na da nasaba da siyasa' — Kalu
Sanatan ya ce matsalolin rashin tsaro da suka addabi Najeriya musamman a yankin Arewa maso Gabas ba haka kawai suke faruwa ba, illa dai wasu na kokarin jefa kasa cikin rudani.
Rahoton Punch ya nuna cewa Sanatan ya ce:
“Wasu daga cikin waɗannan mutane ba wai kudi suke nema ba, iko suke nema. Sun dauki ta’addanci a matsayin hanyar tarwatsa tsarin gwamnati don su hau mulki.”
Kalu ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai don kare martabar kasa, yana mai cewa kamata ya yi a rika fifita jin dadin talaka a maimakon son zuciya.

Asali: Facebook
Sabon hari a Borno ya kashe fasinjoji 9
Zargin Sanata Kalu ya biyo bayan wani hari da Boko Haram suka kai a kauyen Mairari da ke karamar hukumar Guzamala a Borno, inda suka kashe fasinjoji tara.
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya kuma nuna damuwa kan yadda hare-haren ke dawowa cikin jihar, yana mai bukatar gaggauta daukar matakan da suka dace.
Majalisa ta bukaci a inganta tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta bukaci a kara daukan matakan da suka dace domin magance matsalar tsaro.
Hakan na zuwa ne bayan ganin yadda ake samun karuwar kai hare hare a jihohin Taraba, Borno, Benue da sauransu.
Sanata Danjuma Goje ya bukaci a yi bincike mai zurfi domin tabbatar da cewa ba manufar siyasa ce ta sanya kara karfin 'yan ta'adda ba.
Asali: Legit.ng