Ma'aikata Sun Tsunduma Yajin Aiki a Najeriya, An Hana Alkalai Shiga Babbar Kotu
- Yayin da kungiyar JUSUN ta fara yajin aiki, an hana alkalai, lauyoyi da jami'an shari'a shiga kotuna a Ibadan, babban birnin Oyo
- Ma’aikatan JUSUN sun tsunduma yajin aiki a fadin kasar sakamakon gazawar gwamnati na kara albashinsu da 25% da kuma 35%
- Lauyoyi da jama’a sun nuna bacin rai bisa yajin aikin, inda suka yi kira ga gwamnati da ta magance korafe-korafen ma’aikatan shari’a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - A ranar Litinin, jami’an kotu da lauyoyi da masu shari’a sun tarar da kofar kotuna a rufe sakamakon yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) ta fara a Ibadan.
Yajin aikin ya shafi babbar kotun tarayya, kotun daukaka kara da kotun kwadago ta kasa da ke birnin Ibadan, inda aka hana alakalan shiga cikin kotuna gaba ɗaya.

Asali: Getty Images
Ma'aikatan shari'a sun tsunduma yajin aiki
JUSUN ta fara wannan yajin aiki ne a matakin kasa domin neman biyan karin albashi na 25% da 35%, tare da mafi ƙarancin albashi da alawus, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Wani jami’in JUSUN da ke aiki a kotun kwadago ta kasa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa albashinsu yanzu ba ya wadatar da su saboda tsadar rayuwa.
Ya ce ma’aikatan suna cikin mawuyacin hali, kuma alkalai da sauran manyan jami’an shari’a ba sa kallonsu a matsayin abokan aiki.
A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ma'aikacin ya ce, duk matakan da suka ɗauka domin ganin an biya bukatunsu sun ci tura.
Ya ce:
“Ma’aikatan kotun kwadago ta kasa fiye da goma sun mutu daga watan Fabrairun 2025 zuwa yau. Wahala ta yi yawa, kuma ba wai muna neman kari mai yawa ba ne.”
An hana alkalai zaman kotu a Ibadan
Shi ma wani dan kungiyar JUSUN a kotun daukaka kara, Mista Atanda Babatunde, ya ce suna bin umarnin shugabannin kungiyar na kasa ne suka shiga yajin aikin.
Jaridar Vangaurd ta rahoto Babatunde ya bayyana cewa har sai gwamnatin tarayya ta amsa buƙatunsu ne za su ci janye yajin aikin da suka fara.
Wani lauya da ke shirin shiga shari’a a kotun daukaka kara, Mista Ismail Saka, ya bayyana bacin ransa bisa yadda aka hana shiga kotu.
Ya ce an sanar da shi cewa shari’arsa za ta gudana ranar Litinin, amma sai da ya isa ne ya tarar da kofar kotu a rufe saboda yajin aikin JUSUN.

Asali: Twitter
An nemi gwamnati ta biya bukatun JUSUN
Haka zalika, wani Mista Wale Oyegoke da ya kamata a saurari kararsa a babbar kotun tarayya a Ibadan, ya ce yana cikin fushi matuƙa da yadda shari’ar tasa ba ta gudana ba.
Oyegoke ya ce wajibin gwamnati ne ta kula da ma’aikatan bangaren shari’a saboda muhimmancinsu a tsarin mulki da ci gaban kasa.
Ya jaddada cewa tsadar rayuwa a Najeriya ta yi muni, yayin da gwamnati ke samun kuɗi mai yawa daga cire tallafin man fetur.
Ma'aikatan gwamnati sun shiga yajin aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma’aikatan hukumar NiMet sun yi yajin aiki a fadin Najeriya, suna sa ido a filayen jiragen sama don ganin an bi umarninsu.
Sun koka da cewa albashin da ake biyansu bai wadatar ba, har wasu daga cikinsu ke karɓar bashi don biyan haya da kudin makarantar 'ya'yansu.
Shugaban reshen kungiyar, Paul Ogohi, ya ce ma’aikatan NiMet na mutuwa tamkar kaji, inda 70% ke fama da hawan jini, 90% kuma na da matsalar ido.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng