Hako Mai a Arewa: Jihar Neja na Neman Hadaka da Dangote kan Samar da Fetur
- Gwamnan Neja ya nemi kamfanin Dangote da ya saka jari a bincike da haƙar danyen mai a yankin Bida
- Kamfanin Dangote ya tabbatar da cewa yana da shirye-shiryen saka jari sosai a Neja, ciki har da kafa masana'antar shinkafa
- Rahotanni sun ce akwai rijiyoyin mai guda 17 masu amfani da za su iya dorewa har na tsawon shekara 70 a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja ta bayyana bukatar ta na samun haɗin gwiwa da kamfanin Dangote wajen haɓaka albarkatun man da aka gano a yankin Bida.
Gwamna Umaru Bago ne ya bayyana haka yayin taron bikin baje kolin kasuwancin jihar Neja da aka gudanar a Minna.

Asali: Facebook
Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa a shekarun baya a gano cewa akwai albarkatun mai a jibge a jihar Neja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A cewar gwamna Bago, kamfanin Dangote na da cikakkiyar ƙwarewa a harkar makamashi, wanda hakan ya sa ya dace da irin wannan aikin bincike da haƙo mai.
An nemi Dangote ya hako mai a Neja
Gwamnan ya bukaci kamfanoni masu zaman kansu da su shiga aikin bincike da haƙar danyen mai a yankin, yana mai cewa wannan dama ce da za ta kawo bunƙasar tattalin arzikin jihar.
Babban sakataren ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar Neja, Hamza Bello Sarki, wanda ya wakilci gwamnan, ya bukaci Dangote ya hada kai da su wajen hako mai a jihar.
Hamza Bello Sarki ya ce nasarar da Dangote ya samu wajen kafa matatar mai mafi girma a duniya a Najeriya, shaida ce ta ƙwarewarsa.
An gano rijiyoyin mai 17 a jihar Neja
This Day ta wallafa cewa binciken shekarar 2023 ya nuna cewa akwai rijiyoyin mai 17 a jihar Neja da za su iya samar da mai na tsawon shekara 70.
Yankin Bida na daga cikin yankunan da ke cike da albarkatun mai, wanda ya ratsa tsakanin jihohin Neja da Kwara, kuma gwamnatin na fatan hakan zai zama tushen ci gaba.
Dangote na da shirin zuba jari a Neja
Wakilin kamfanin Dangote, Hashem Ahmed, ya bayyana cewa suna da shirin saka jari sosai a jihar Neja, ciki har da kammala kamfanin casar shinkafa a Wushishi.
Ya ce Dangote zai rika sayen shinkafa har tan miliyan 1 a duk shekara, wanda hakan zai ƙarfafa manoma da saka jari daga wasu kamfanoni.
Ahmed ya jinjinawa gwamna Bago kan manufofin sa da suka ƙunshi kafa yankin kasuwanci na musamman domin jawo masu zuba jari da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

Asali: Facebook
Ya ce wannan mataki na gwamnati zai samar da wani ingantaccen yanayi ga masana'antu da manoma a jihar Neja, tare da kara jan hankalin masu saka jari daga ko'ina.
Habaka tattali: Dangote zai zuba jari a Taraba
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin zuba jari a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas.
Aliko Dangote ya bayyana haka ne yayin wani taron tattalin arziki da gwamnatin Taraba ta shirya a Jalingo.
Taron da ya gudana a watan da ya gabata ya hada manyan 'yan kasuwa da shugabanni ciki har da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Asali: Legit.ng