Hajjin Bana: Za a Fassara Hudubar Arfah zuwa Hausa, Fulatanci da Sauran Harsuna 32

Hajjin Bana: Za a Fassara Hudubar Arfah zuwa Hausa, Fulatanci da Sauran Harsuna 32

  • An bayyana kudurin fassara hudubar hajjin bana zuwa harsuna sama da 30, ciki har da manyan harsunan Najeriya guda uku
  • A halin da ake ciki, mahajjata a Najeriya da sauran kasashe na shirin ibada a kasar Saudiyya, za a yi hudubar Afrah a ranar 5 ga Yuni
  • Aikin Hajjin bana ya zo da sabon salo a Najeriya, inda ake kukan tsawwala kudin jirgi zuwa Saudiyya ba kamar yadda aka saba ba

Jihar Edo - Daular Saudiyya ta bayyana cewa za a fassara hudubar Arafah ta shekarar 2025 kai tsaye cikin harsuna 34, ciki har da manyan harsunan Najeriya guda uku; Hausa, Fulatanci da Yarbanci.

Shugaban Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Musulmi ta Jihar Edo, Malam Musah Muhammad-Uduimoh ne ya bayyana hakan a wata hira da NAN a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa sanarwar ta fito ne daga Ofishin Shugabancin Kula da Al’amuran Addini na Masallatai Masu Alfarma guda biyu a Saudiyya, a ranar Asabar.

Hajjin bana da harshen Hausa
Hausa da Fulani za su fahimci hudubar Arfah | Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

Fa’idar hudubar a harsunan gida

Muhammad-Uduimoh ya bayyana wannan sabon tsari a matsayin babban ci gaba wajen samar da fahimta da haɗin kai a tsakanin musulmi, musamman ga mahajjata daga Najeriya da ke amfani da harsunan da aka ambata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ya ce wannan dama za ta bai wa mahajjata damar fahimtar hudubar Arafah da ke ɗauke da sakonni masu zurfi da muhimmanci cikin yaren da suke fahimta sosai, Premium Times ta ruwaito.

A cewarsa

“A wannan shekara, za a tabbatar da cewa duk musulmi da ke wajen hudubar za su iya jin saƙon da ke cikinta cikin yaren da suka saba da shi. Wannan babbar dama ce ga jama’armu da ke magana da Hausa, Fulatanci da Yarbanci.”

Yaushe za a yi hudubar Arfah a 2025?

Ya ƙara da cewa fahimtar hudubar Arafah a cikin yaren mutum na gida zai sanya saƙon addini ya zama mafi tasiri, ya fi shafar zuciya, kuma zai taimaka wajen canja halaye da ƙarfafa imani.

Ya kara da cewa:

“Lokacin da mutum ya fahimci huduba cikin harshen da ya san shi sosai, to saƙon zai shige zuciyarsa kai tsaye, kuma hakan na ƙarfafa haɗin kan al’umma musulmi a duniya baki ɗaya.”

An ruwaito cewa za a gabatar da hudubar Arafah a ranar 5 ga watan Yuni, kuma babban limamin Masallacin Harami a Makkah, Sheikh Bin Humaid ne zai gabatar da ita daga Masallacin Namirah.

Su wa za su amfana da hudubar Arfah?

Ana sa ran za a watsa hudubar ta kai tsaye ga miliyoyin musulmi a faɗin duniya kamar yadda aka saba duk shekara.

Hudubar Arafah na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan aikin Hajji, kuma ana kallonta a matsayin kololuwar ibada, musamman a lokacin da mahajjata ke taruwa a filin Dutsen Arafah don neman rahamar Allah da jinƙai.

Hajjin bana za a yi Arfah da Fulatanci
Za a yi hudubar Arfah da Fulatanci | Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

Haka zalika, Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Edo, Abdulkabir Muhammadkabir, ya yaba da wannan mataki daga Saudiyya.

Ya ce wannan sabuwar hanya za ta ƙara zurfafa kaimin ibada da dangantakar mahajjata da saƙon Musulunci a duniya.

Halin da mahajjata ke ciki a yanzu

A cewarsa, wannan mataki zai sa hudubar ta zama ba wai kawai abin sauraro ba ne, sai dai ta zama abin da ke shiga kai tsaye zuwa zukatan mahajjata.

A halin yanzu, mahajjatan daga Najeriya da sauran kasashen duniya na ci gaba da gudanar da ibadunsu a Saudiyya.

Hakazalila, ana sa ran za su haɗu da gaba daya a Dutsen Arafah domin yin hudubar Arafah wadda ke matsayin muhimmin abin tarihi a Hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

OSZAR »