Fitattun Ƴan Wasan Kano 21 Sun Mutu a Hanyar Komawa Gida daga Jihar Ogun
- Yan wasan Kano 21 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar dawowa daga jihar Ogun yau Asabar
- Rahotanni sun bayyana cewa ƴan wasan sun gamu da ajalinsu ne bayan sun halarci gasar wasanni wacce aka yi a jihar Ogun
- Wani jami'in hukumar wasanni ta Kano, Ado Salisu ya ce mutum 19 suka mutu nan take, yayin da biyu suka cika a asibiti
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Akalla ’yan wasa da jami’an Kano guda 21 da suka wakilci jihar a gasar wasanni ta kasa da aka kammala a Jihar Ogun sun rasu a wani mummunan hadarin mota a safiyar Asabar.
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na safiyar yau Asabar, a gadar Daka Tsalle da ke yankin ƙaramar hukumar Garun Malam a jihar Kano.

Asali: Twitter
Shaidu sun tabbatar wa da Daily Nigerian cewa mutane sama da goma sun jikkata matuka, yayin da wasu suka rasu nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Motar da ta yi hatsarin dai ta ɗauko fasinjoji 35 waɗanda suka kunshi yan wasa da jami'an hukumar wasannin Kano.
Ƴan wasan Kano 21 sun mutu a hatsari
Ado Salisu, daya daga cikin jami’an da ke cikin tafiyar, ya bayyana cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safe a gadar Daka Tsalle, lokacin da motar bas din da suka ke ciki ta taka rami ta faɗa ƙasan gadar.
Ado Salisu ya ce mutum 19 sun rasu a wurin hadarin nan take, yayin da karin biyu suka rasu a Asibitin Kura.
Daga cikin wadanda suka rasu akwai Galadima Ibrahim, mai magana da yawun Hukumar Wasanni ta Jihar Kano.
Ya kara da cewa wadanda suka jikkata na ci gaba da samun kulawa a asibiti, yayin da ake shirin mika gawawwakin waɗanda suka rasu ga iyalansu domin yi masu jana’iza.

Asali: Facebook
Hatsarin ya girgiza mutanen Kano
Rahotanni sun ce motocin Kano guda 30 da suka dauko sauran ’yan tawagar daga Ogun sun bar jihar Ogun tun a daren Alhamis kuma sun isa Kano lafiya.
Wannan hadari ya girgiza daukacin al’ummar Kano, musamman ma’aikata da magoya bayan wasanni, inda mutane da dama ke bayyana jimami da alhinin su kan wannan babban rashi da jihar ta yi.
Ana sa ran gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace domin taimakawa iyalan wadanda suka rasu da kuma kula da wadanda suka jikkata, rahoton Leadership.
Babbar mota ɗauke da ragunan layya ta kife
A wani labarin, kun ji cewa wata babbar mota da ta ɗauko raguna da shanun layya daga jihar Kebbi ta gamu da mummunan hatsari a jihar Osun.
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen Osun, Agnes Ogungbemi, ta ce mutane biyu, maza, sun mutu a hadarin, yayin da 15 suka jikkata sakamakon hatsarin.
Wani shaida mai suna Emmanuel Adegboye ya ce hadarin ya faru ne a kusa da Oke-Ofa da ke yankin Gbongan, lokacin da motar ta ci ƙarfin direban, ta faɗa rami.
Asali: Legit.ng