Gwamnatin Najeriya za Ta Kafa Kotun Hukunta Dalibai Masu Satar Amsa
- Gwamnatin Tarayya na shirin kafa kotu ta musamman domin hukunta masu satar amsa a lokacin jarrabawa a fadin Najeriya
- Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya ce za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin Farfesa Ishaq Oloyede ya gabatar, ciki har da kafa kotu ta musamman
- Kwamitin ya kuma bukaci a rika amfani da lambar NIN da kyamarori na CCTV a cibiyoyin jarrabawa domin hana magudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta kafa kotu ta musamman domin gurfanar da duk masu hannu wajen satar amsa a lokacin jarrabawa a makarantu.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya fadi haka a Abuja yayin karɓar rahoton kwamitin da ke duba hanyoyin inganta jarrabawa a Najeriya da shugaba JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ke jagoranta.

Asali: Twitter
Punch ta rahoto cewa Ministan ya tabbatar da cewa dukkanin shawarwari 12 da kwamitin ya gabatar za a aiwatar da su gaba ɗaya domin kawo karshen matsalar satar amsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Za a kafa kotun barayin amsa a Najeriya
Daya daga cikin muhimman shawarwarin kwamitin shi ne bukatar kafa kotu ta musamman da za ta yi hukunci cikin gaggawa kan barayin amsa.
Kwamitin ya bukaci ma’aikatar ilimi ta tuntubi Majalisar Dokoki domin samar da dokar kafa wannan kotu.
The Guardian ta wallafa cewa ministan ya ce:
“Zan tabbatar muku da cewa dukkan shawarwarin da kuka bayar za mu aiwatar da su. Babu wanda ba za a iya aiwatarwa ba. Za mu fara da wanda ya dace nan take.”
Kwamitin ya ce kafa kotun zai zama wata babbar hanya ta hana wasu shiga harkar satar amsa da ke lalata ingancin ilimi a ƙasar.
Za a rika amfani da NIN yayin jarrabawa
Kwamitin ya bada shawarar hada bayanan ɗalibai kamar haɗa bayanan da NIN, hoton da ranar haihuwa domin hana wasu zama sojojin gona.
Haka kuma, an bukaci duk cibiyoyin jarrabawa za su rika amfani da kyamarorin CCTV domin sa ido a lokacin jarrabawa.
Kwamitin ya bukaci cewa duk masu sa ido da masu kula da jarrabawa su kasance ma’aikatan gwamnati kuma su rika rajista da NIN kafin su shiga aikin.
Za a fara jarrabawar kwamfuta daga 2025
Kwamitin ya kuma bukaci fara amfani da jarrabawar kwamfuta (CBE) tun daga 2025 ga ɗaliban makarantu masu zaman kansu, sannan daga 2026 ga ɗaliban makarantun gwamnati.
Sannan ya bukaci a sake duba tsarin tattara sakamakon dalibai, yana mai cewa an riga an mayar da shi hanyar satar maki da cin hanci a wasu makarantu.
Kwamitin ya ce dole a gyara dokar hana satar amsa ta shekarar 1999 saboda rashin aiki da ita ko rashin niyyar aiwatar da ita, domin samar da doka mai ƙarfi da za a iya aiki da ita nan take.

Asali: Facebook
Za a fara dakatar da barayin amsa a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa ministan ilimin Najeriya ya ce za a fara hukunta wadanda aka kama suna satar amsa.
Dr Tunji Alausa ya ce za a fara dakatar da duk dalibin da aka kama da satar amsa daga rubuta jarrabawa na tsawon shekara uku.
Ma'aikatar ilimi ta kasa ta bayyana cewa daukar matakin zai taimaka wajen bunkasa ilimi da hana dalibai satar amsa a Najeriya.
Asali: Legit.ng