Matashi Ya Saya wa Tinubu Ragon Layya, Ya Yi wa Mamar Shugaban Kasa Mai Suna
- Wani matashi daga jihar Bauchi ya bai wa Shugaba Bola Tinubu ragon Sallah a matsayin godiya kan bayar da lasisin aikin mai na Kolmani
- Ya bayyana cewa wannan lasisi zai kawo ci gaban tattalin arziki da damammaki ga Arewacin Najeriya da ma kasa baki ɗaya
- Khamis Musa Darazo ya ce yana nuna ƙauna ta musamman ga Tinubu tun kafin ya hau mulki, har ya sa wa 'yarsa sunan mamar shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da bikin babbar Sallah ke karatowa, wani matashi mai suna Khamis Musa Darazo daga jihar Bauchi ya bayar da kyautar ragon Sallah ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Khamis ya ce wannan sadaukarwa ce ta nuna farin ciki da godiyarsa ga shugaban bisa amincewa da bayar da lasisin aikin hakar mai a yankin Kolmani.

Asali: Facebook
Binciken Legit ya tabbatar da cewa Khamis Musa Darazo ya wallafa hoton shi tare da ragon a shafin shi na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
A kwanakin baya ne ministan, Sanata Heineken Lokpobiri ya sanar da amincewar gwamnatin Tinubu da duk wasu takardun lasisin da ake bukata don hako mai a Kolmani.
Muhimmancin hako mai a Kolmani
Aikin mai na Kolmani da ya shafi iyakokin jihohin Bauchi da Gombe, na daya daga cikin manyan ayyukan da ake sa ran zai kawo sauyi a fannin tattalin arziki a Arewacin Najeriya.
Khamis ya bayyana cewa amincewa da wannan aiki da gwamnati ta yi zai ƙara buɗe ƙofofin kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa da sauran jama’a a Arewa da ma Najeriya.
'Na sadaukar da rago ga Tinubu' – Khamis
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, Khamis ya ce ragon da ya bayar kyauta ce ta musamman domin nuna godiyarsa ga shugaban kasa.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa matashin ya ce:
“Ina mika matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu bisa wannan dama da ya bai wa Arewa.
"Aikin Kolmani zai kawo ci gaba da dama, kuma hanyar da na fi ganin ya dace in nuna farin cikina ita ce ta bayar da ragon Sallah.”
Khamis ya yi mai suna wa mamar Tinubu
Khamis ya bayyana cewa yana daga cikin magoya bayan Tinubu tun kafin ya zama shugaban ƙasa, har ma ya sadaukar da alawus ɗin hidimar ƙasa (NYSC) lokacin kamfen ɗin sa.
Har ila yau, ya bayyana cewa ya sa wa 'yarsa sunan mahaifiyar shugaban ne saboda ƙaunar da yake wa dangin Tinubu da irin tasirinsu a rayuwarsa.
A ƙarshe, Khamis ya yi addu’ar Allah ya taimaka wa Shugaba Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka ga ‘yan Najeriya, musamman ma na kawo sauyi a fannin tattalin arziki da raya ƙasa.
An saya wa gwamnan Gombe ragon layya
A wani rahoton, kun ji cewa talakawa a jihar Gombe sun saya wa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ragon layya.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen unguwar Nayinawa ne suka saya wa gwamnan ragon saboda aikin da ya musu.
Dan Majen Nayinawa ya zantawa Legit cewa mutanen unguwar ne suka hada kudi domin sakawa gwamnan saboda aikin da ya musu.
Asali: Legit.ng